Sarki Sanusi II Ya Kai Ziyarar Bazata ga Gwamna a Arewa, Ya Shiga Gidan Marayu

Sarki Sanusi II Ya Kai Ziyarar Bazata ga Gwamna a Arewa, Ya Shiga Gidan Marayu

  • A yau Juma'a 13 ga watan Disambar Sarki Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya
  • Yayin ziyarar, basaraken ya je gidan marayu da ke birnin Jos kafin kaiwa Gwamna Caleb Mutfwang ziyara ta musamman
  • Wannan na zuwa ne mako daya da barkewar rikicin sarauta a ranar Juma'a 6 ga watan Disambar 2024 a kan masarautar Bichi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara ta musamman a jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Gwamna Caleb Mutfwang na jihar a gidan gwamnati inda suka zanta kan wasu batutuwa.

Sanusi II ya ziyarci Gwamna a gidan gwamnati
Sarki Sanusi II ya gana da Gwamna Caleb Mutfwang a Plateau. Hoto: MAJEEDA STUDIO.
Asali: Facebook

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan marayu

Shafin Masarautar Kano ne ya wallafa hakan a manhajar X a yau Juma'a 13 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yanke shawara bayan jami'an tsaro sun hana shi zuwa Bichi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko kafin kai wa gwamnan ziyara, Sarki Sanusi II ya ziyarci gidan marayu da ke garin Jos babban birnin Plateau.

Sanusi II Dynasty ya wallafa a shafin Facebook cewa Sarki Sanusi II ya samu rakiyar Sarkin Wase.

Wadanda suka raka Sarki Muhammadu Sanusi II

Sauran wadanda suka raka basaraken sun hada da hakimai da wasu khalifofin darikar Tijjaniya.

Daga cikin malaman da suka samu raka Sarki Sanusi II ziyarar akwai Sheikh Harisu Jos da Sheikh Shehi Mai Hula da sauransu.

A cikin faifan bidiyo, an gano Sanusi II a gidan marayu na 'ANWARUL Faidah Orphanage' da ke kan hanyar Kazaure a Jos.

Sarki Sanusi II ya magantu kan rigimar sarauta

Kun ji cewa Mai Martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce har yanzun ba shi da masaniyar dalilin jami'an tsaro na mamaye fadarsa a makon jiya.

Sanusi II ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wakilan masarautar Bichi da suka kai masa ziyara ranar Laraba 11 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna na kuntatawa 'yan majalisu masoyan tsohon gwamna? hadiminsa ya magantu

Sarkin ya ce ko ma menene dalilin waɗanda suka sa a mamaye fadar, ba zai hana shi raka hakimin Bichi masarautarsa ba a ranar da zai sake sanyawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.