Tinubu Ya Yi wa Barau Gata, Baki Sun Cika Abuja domin Halartar Bikin, An Yada Hotunan Aure
- Manyan 'yan siyasa da dattawa sun halarci bikin daurin auren yar Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja
- An daura auren me tsakanin iyalan Barau da na tsohon Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero a masallacin Abuja
- Tinubu shi ne ya kasance waliyyi ga ya'yan Sanata Barau duka biyu ta hannun Hon. Tajudden Abbas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - A yau Juma'a 13 ga watan Disambar 2024 aka daura auren yar gidan Sanata Barau Ibrahim Jibrin.
An daura auren karkarshin jagorancin babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari.
An daura auren yar Sanata Barau Jibrin
Daily Trust ta wallafa hotunan daurin auren inda shugaban kasa Bola Tinubu ya zama babban bako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran manyan da suka halarci bikin daurin auren akwai kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon Tajuddeen Abbas, da shugban APC, Abdullahi Ganduje da gwamnonin jihohi da sanatoci.
Sai kuma ɗan uwa ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura, sun kasance daga cikin manyan baki.
An daura auren ɗan Sanata Barau, Jibrin Barau I Jibrin da Maryam Nasir Ado Bayero, ‘yar tsohon Sarkin Bichi.
Sai kuma Aisha Barau I. Jibrin da Injiniya Abubakar, ɗan Dr Abdulmunaf Yunusa Sarina, shugaban kamfanin Azman.
Tinubu ya ba da auren 'ya 'yan Barau Jibrin
Shugaba Tinubu ya yi wa 'ya'yan Sanata Barau biyun wakilci da waliyyanci ta hannun kakakin Majalisar Wakilai a cewar Punch.
Haka kuma, Ganduje ya kasance waliyyin Maryam, 'yar Ado Bayero, yayin da Sanata Tanko Al-Makura, ya kasance wakili na Injiniya Abubakar.
Gwamnonin da suka halarci bikin sun haɗa da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq da Gwamna Peter Mbah na Enugu da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Sauran sun hada da Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda da Gwamna Ahmed Usman Ododo na Kogi da Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da sauransu.
An sauya wurin daurin auren 'yar Barau
A baya, kun ji cewa kwanaki kadan kafin daurin auren iyalan Nasir Ado Bayero da Sanata Barau Jibrin, an canza wurin daurin auren daga Kano zuwa Abuja.
Mutane da dama sun yi ta alakanta daukar matakin da cewa akwai siyasa a ciki duba da ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji.
Sai da iyalan amarya sun fitar da sanarwa ta musamman domin fayyace gaskiya kan dalilin canza wurin auren zuwa birnin Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng