Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban NCoS bayan Karewar Wa'adin Haliru Nababa
- Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Nwakuche Ndidi a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali
- Hakan ya biyo bayan karewar wa'adi da kuma ritayar tsohon shugaban hukumar, Haliru Nababa wanda Muhammadu Buhari ya naɗa a 2021
- Sabon muƙaddashin shugaban zai fara aiki ne daga ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba, 2024 kamar yadda sanarwa ta tabbatar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Nwakuche Ndidi a matsayin mukaddashin Konturola-Janar na hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS).
Shugaba Bola Tinubu ya yi wannan naɗi ne sakamakon ƙarewar wa'adin Konturola Janar na yanzu, Haliru Nababa.
Sakataren hukumar kula da hukumomin NSCDC, kashe gobara, shige da fice da gyaran hali ta Najeriya, Ja’afaru Ahmed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne ya naɗa Haliru Nababa ranar 18 ga watan Fabrairun 2021, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugaba Tinubu ya naɗa shugaban NCoS
"Shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da nadin Nwakuche Sylvester Ndidi a matsayin mukaddashin Konturola Janar na hukumar gyaran hali.
"Shugaban ya yi wannan naɗi ne biyo bayan karewar wa'adin Haliru Nababa. Sabon shugaban hukumar gyaran halin zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba."
- Ja'afaru Ahmed.
Takaitaccen bayani kan sabon konturolan NCoS
An haifi Nwakuche Ndidi a ranar 26 ga Nuwamba, 1966 a yankin Oguta da ke jihar Imo. a Kudu maso Gabashin Najeriya, cewar Daily Trust.
Gabanin wannan naɗi da aka yi masa, shi ne mataimakin konturola janar mai kula da sashen ba da horo da kula da ma'aikata.
Shugaban ƙasa Tinubu ya buƙaci sabon shugaban hukumar gyaran halin ya yi amfani da gogewarsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Tinubu ya naɗa mukaddashin Akanta-Janar
Ku na da labarin shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da nadin sabon mukaddashin Akanta-janar na Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Sanarwar da aka fitar ta ce Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi ne saboda kwarewar da yake da shi kan lissafe-lissafen kudi a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng