Jerin Abubuwa 6 da Gwamnatin Tinubu za Ta yi wa 'Yan Najeriya a Shekarar 2025
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon shirin da ta yi wa matasa ana kokarin shiga 2025 domin samar da ayyuka da karfafasu
- Ministan matasa, Ayodele Olawande ya bayyana cewa gwamnati ta kafa cibiyoyi da tsare-tsare don taimakawa tattalin matasa
- Legit ta tattauna da wani shugaban matasa domin jin yadda suka shirya wajen tabbatar da sun ci gajiyar shirin da ake kokarin kawowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na ci gaban matasa a shekarar 2025 da nufin samar da ayyukan yi.
An sanar da shirin ne yayin rufe taron kasa na cigaban matasa karo na bakwai (NCYD) a Jihar Borno.
Ministan matasa, Ayodele Olawande, ya wallafa a Facebook cewa matasa suna da rawar da za su taka wajen cigaban tattalin arzikin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tanadin da aka yi wa 'yan Najeriya a 2025
Vanguard ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana manyan tsare-tsare guda shida domin bunkasa ci gaban matasa a 2025:
1. Samar da jari
2. Samar da ayyuka
3. Horaswar sana’o’i
4. Tallafin kasuwanci
5. Shirin karfafa matasa
6. Shigar da matasa harkokin gwamnati
Shirin kafa cibiyoyin taimakon matasa
Hon. Ayodele Olawande ya bayyana cewa an samar da kafar Youth Help Desk domin taimaka wa matasa da sauraron korafe-korafensu kai tsaye.
Haka zalika, gwamnati ta amince da kafa cibiyoyin matasa a Abuja, jihohi da dukkan kananan hukumomi 774 domin tallafa musu ta hanyoyi daban-daban.
Zulum zai cigaba da taimakon matasa
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa matasa ta hanyar horaswa na sana’o’i, ilimi da bayar da tallafin karatu.
Farfesa Zulum ya kara da cewa matasa ne ginshikin tattalin arzikin kasa, saboda haka akwai bukatar a tallafa musu domin su zama masu tasiri a al’umma.
Legit ta tattauna da Usman Sai'du
Wani jagoran kungiyar matasa a jihar Gombe, Usman Sa'idu ya ce za su rika bibiya wajen sanin halin da ake ciki a kan shirye shiryen.
Bayan haka, ya ce idan abubuwa suka kankama, za su wayar wa matasa kai a kan yadda za su ci gajiyar shirin.
Tinubu zai ba da tallafin lafiya ga 'yan kasa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce tana cikin shirye-shirye wajen sayen magungunan asibiti domin saukakawa al'umma.
Ministan lafiya na kasa, Farfesa Muhammad Pate ya ce an samar da karin dala biliyan 3 domin tallafawa kiwon lafiya a shekaru masu zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng