Majalisa Ta Fito da Bayani kan Rage Karfin Ikon Lamidon Adamawa

Majalisa Ta Fito da Bayani kan Rage Karfin Ikon Lamidon Adamawa

  • Majalisar dokokin Adamawa ta musanta wasu daga cikin abubuwan da aka ce su na cikin sabuwar dokar masarauta
  • Tun da fari, an yi zargin cewa dokar ta na kokarin rage karfin ikon Lamidon Adamawa a matsayin shugaban sarakuna
  • Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin bayanai, Hon. Musa Mahmud ya fadi gaskiyar abin da dokar ta kunsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - Majalisar dokokin Adamawa ta karyata wani ikirarin a kan sabuwar dokar da ta kafa karin masarautu, wacce gwamna Ahmadu Fintiri ya gabatar masu.

An samu rahoton cewa dokar na da niyyar cire Lamidon Adamawa daga matsayin shugaban majalisar gargajiya ta jihar.

Fintiri
An yi bayanin dokar masarautar Adamawa Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kwamitin majalisar kan harkokin bayanai, Alhaji Musa Mahmud, ne ya yi ƙarin haske a kan abin da dokar ta kunsa.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta kashe bashin $232m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamawa ta yi bayani kan sabuwar dokar masarauta

Hon. Musa Mahmud wanda ke wakiltar Mazabar Mayo-Belwa, ya musanta zargin cewa akwai makrkashiyar rage ikon Lamidon Adamawa.

Ya bayyana cewa;

“Sashe na 18, sakin layi na biyu ya bayyana cewa: Lamidon Adamawa zai kasance shugaban Majalisar Gargajiya ta Jihar Adamawa.”

Musa Mahmud ya ce wannan sashe ya tabbatar wa da Lamidon Adamawa ikonsa kamar yadda ya ke a baya na zama shugaban majalisar sarakunan jihar

Dan majalisa ya fayyace dokar masarautar Adamawa

Mahmud ya bayyana cewa sabon abu da aka kara a dokar shi ne kafa majalisun gargajiya na yankuna guda uku; wannan ta haɗa da na yankin Arewa, Tsakiya da Kudancin Jihar. Ya bukaci al’ummar jihar su yi watsi da bayanan karya da masu yada jita-jita ke yayatawa na kokarin rage ikon Lamidon Adamawa.

Adamawa: Majalisa ta daga likkafar sarakuna

A wani labarin, kun ji cewa majalisar dokokin Adamawa ta karbi kudirin gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri domin daga likkafar wasu daga cikin sarakunan gargajiya.

Kara karanta wannan

Gwamna na kuntatawa 'yan majalisu masoyan tsohon gwamna? hadiminsa ya magantu

An yi zargin dokar za ta rage karfin ikon Lamidon Adamawa a matsayin shugaban majalisar sarakuna, tare da jujjuya mukamin a tsakaninsu domin samun daidaito.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.