Naira: Masu POS Sun Canza Hanyar Neman Tsabar Kuɗi, Sun Kara Takurawa Ƴan Najeriya

Naira: Masu POS Sun Canza Hanyar Neman Tsabar Kuɗi, Sun Kara Takurawa Ƴan Najeriya

  • Karancin Naira ya ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahala yayin da masu POS suka ƙara kuɗin caji saboda wahalar samun kuɗi
  • An ruwaito cewa bankuna sun daina ba da tsabar kudi yadda ya kamata, galibi sun rage adadin cire kuɗi zuwa N5,000 a rana
  • Wasu masu sana'ar POS sun shaida mana cewa a yanzu sun koma neman tsabar kudi wurin ƴan kasuwa da gidajen mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Matsalar karancin Naira na ƙara ƙamari a Najeriya domin a yanzu bankuna da dama sun daina ba masu POS tsabar kuɗi yadda ya kamata.

Galibin masu sana'ar POS sun koma neman tsabar kudi daga wurin ƴan kasuwa da gidajen mai saboda bankuna sun rage adadin cire kudi zuwa N5,000.

Masu POS.
Karancin kuɗi ya kara jefa masu POS cikin wahala, sun koma neman tsabar kudi a gidan mai Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Binciken Daily Trust ya nuna cewa masu POS suna biyan N1,000 zuwa N2,000 don siyan tsabar kudi daga N100,000-N200,000 a wurin ƴan kasuwa ko gidajen mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu POS sun kara kuɗin da ake karba

Wannan dalili ya sa masu POS suka nunka kuɗin da suke cajin kwantomomi masu zuws cire kuɗi don amfanin yau da kullum.

Alal misali, kuɗin cire N5,000 a wurin mai POS a yanzu ya tashi daga N100 zuwa N200, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Wani mai POS ya nuna damuwa game da matsalar ƙarancin kuɗi, yana mai cewa a yanzu ba a samun isassun Naira a bankuna da na'urorin cire kudi watau ATMs.

Halin da masu POS suka shiga

Wata mai sana'ar POS, Beauty Odion ta bayyana cewa a yanzu sun koma yawon neman tsabar kudi a lokacin da ya kamata a ce suna zaune a wuraren sana'o'insu.

"Yanzu saboda ƙarancin kudi, da sassafe muke barin gida mu tafi yawon neman tsabar kudi, tun karfe 11:00 na safe har 12:00 muna abu ɗaya."
"Wani lokacin sai na je bankuna huɗu zuwa biyar neman kuɗi a ATM, kuma idan aka ci sa'a ana samu," in ji ta.

Wani mai POS, Abdulbasi Salisu ya shaidawa Legit Hausa cewa ya daina zuwa banki neman tsabar kuɗi saboda ya san ba zai samu abin da yake so ba.

A cewarsa yana samun kudi a yanzu daga hannun ƴan kasuwa da masu shaguna, inda ya kara cewa cajin da ake wa mutane ya ƙaru.

"Ana karancin kudi sosai, ni dai na fi mako biyu ban je banki ba, ina da abokai da yayye ƴan kasuwa da suke ma'amala da tsabar kuɗi."
"Mun kuma kara kuɗin caji saboda wahalar samun kuɗin, maimakon N200 a cire N20,000, yanzu har N500 muna karba," in ji shi.

Majalisa ta sa baki kan karancin Naira

Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta sa baki kan ƙarancin takardun kudin da ake fama da shi a ƴan kwanakin nan a Najeriya

A zaman ranar Talata, 10 ga watan Disamba, majalisar ta bukaci bankin CBN ya magance matsalar cikin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262