Jagoran PDP Ya Fadi Wanda Ake Amfani da Shi domin Rusa Jam'iyyar Adawa

Jagoran PDP Ya Fadi Wanda Ake Amfani da Shi domin Rusa Jam'iyyar Adawa

  • Jigo a PDP, Tonye Cole ya ce babu boye-boye a cikin aikin da Nyesom Wike ke yi wa jam'iyya mai mulki ta APC
  • Tonye Cole ya fusata da yadda duk da kowa ya san rawar da Wike ke takawa a PDP, amma an gaza taka masa birki
  • Ya bayyana cewa baya ga PDP, APC ta na sane da aikin da ta dauki Wike ya yi mata a cikin jam'iyyarsa ba tare da boye-boye ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaDaya daga cikin jagororin PDP, Tonye Cole ya bayyana irin illar da zaman Nyesom Wike ke yi wa jam’iyyar hamayya a kasar nan.

Mista, wanda ya kafa Sahara Group da shi ya kara da cewa babu wanda bai san irin kalubalen da Ministan babban birnin tarayya ke yi wa PDP ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin fitacciyar jarumar Kannywood da neman mata? Ƴar TikTok ta ƙaryata kanta

Nyesom
Jagoran PDP ya zargi Wike da yi wa APC aiki Hoto: Nyesom Ezonwo Wike CON
Asali: Facebook

Tonye Cole, ta cikin shirin untold stories ya ce jam’iyyar PDP na cikin rikici tun bayan da Wike ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jam'iyyar APC na amfani da Nyesom Wike," Cole

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Tonye Cole, wanda ya tsaya takarar gwamna karkashin APC a jihar Rivers a zaɓen 2023, ya ce jam’iyya mai mulki da kuma Wike sun a kokarin durkusar da jam’iyyar adawa.

“Ba a boye ba ne ga kowa; ba a ɓoye ba. Matsayin da yake takawa yanzu a PDP shi ne raunana ta har ta kai ba za ta iya zama babbar ƙalubale ga APC a nan gaba ba,”

An zargi PDP da gaza maganin Wike

Tsohon 'dan takaran na PDP, ya zargi jam’iyyarsa da gaza tabuka komai a kan yadda Nyesom Wike ke abin da ya ga dama na durkusar da ita.

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu: APC ta fadi abin da zai faru da Atiku, Obi a zaben 2027

“PDP ta san da wannan. Kowa ya san da wannan. APC ta san da wannan. Kowa ya san da wannan. Shi ma (Wike) ya san da wannan."

Ya bayyana mamaki matuka, ganin yadda da kansa Nyesom Wike bai boye manufarsa ta raunata tasirin PDP a siyasar kasar nan.

Gwamna ya musanta sauya sheka daga APC

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Filato, Caleb Muftwanga ya magantu a kan rahoton da ake yadawa na cewa ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC.

Gwamna Muftwanga ya yi Allah-wadai da wani hoto da ke zagayawa inda aka ce an gan shi da gwamnonin APC su na jiran shugaban kasar nan, Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.