Tsohon Gwamnan Kogi Ya Faɗawa Kotu Abin da Ya Sani kan Zargin Karkatar da N80bn
- Yahaya Bello ya musanta tuhumar da ake yi masa ta karkatar da Naira biliyan 80 daga asusun gwamnatin Kogi a lokacin mulkinsa
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan tuhume-tuhume 19 na zamba
- Sai dai a zaman kotun yau Juma'a, 13 ga watan Disamba, Mai shari'a Emeka Nwite ya karɓi uzurin lauyan EFCC na janye wata buƙata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya shaidawa kotu cewa ba shi da hannu a tuhumar karkatar da Naira biliyan 80 daga baitul-mali a lokacin mulkinsa.
Yahaya Bello ya musanta tuhumar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa watau EFCC take masa na karkartar da waɗannan kuɗaɗe a zaman babbar kotun tarayya.
Tsohon gwamna ya musanta zargin EFCC
Channels tv ta tattaro cewa EFCC ya gurfanar da tsohon gwamna a gaban Mai shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar yaƙi da rashawar ta shigar da tuhume-tuhume 19 kan Yahaya Bello wanda dukkansu sun shafi zargin wawure N80bn daga baitul-malin jihar Kogi.
Yayin da aka dawo zaman shari'ar yau Juma'a, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, SAN, ya janye bukatar da ya shigar tun farko na matso da ranar gurfanar da wanda ake tuuma.
Ya shaidawa kotun cewa ɓukatar ta ci karo da abubuwan da suka faru a dangane da shari'ar.
A nasa ɓangaren lauyan wanda ake ƙara, Joseph Daudu, SAN, bai yi jayayya da matakin da lauyan EFCC ya ɗauka ba.
Kotu ta yi fatali da bukatar hukumar EFCC
Daga nan Mai shari'a Justice Emeka Nwite ya amince da janyewar kuma ya yi watsi da bukatar.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a baya EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo saboda rashin mutunta sammacin da ta aika masa, daga baya ta cafke shi.
Dino Melaye ya tsokani Yahaya Bello
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Dino Melaye ya taso tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gaba bayan kotu ta tura shi gidan gyaran hali na Kuje.
Tsohon sanatan ya bayyana cewa dama a baya ya taɓa yin hasashen cewa Yahaya zai ƙare a gidan kaso idan ya kammala mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng