Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Sayen Magani ga 'Yan Najeriya

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Sayen Magani ga 'Yan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce tana cikin shirye-shiryen hadin-guiwar siyan magungunan asibiti domin tabbatar da inganci da saukaka rayuwa
  • Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya ce an samar da karin dala biliyan 3 domin tallafawa kiwon lafiya daga 2024 zuwa 2026
  • Gwamnati ta yi alkawarin inganta samar da inshorar lafiya ga marasa galihu da kuma kara yawan magunguna da kayan aikin asibiti

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na sayen magunguna domin magance karuwar farashin magani da sauran kayayyakin kiwon lafiya a Najeriya.

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya ce wannan shiri wani bangare ne na ƙoƙarin rage radadin farashin kayan kiwon lafiya ga al’umma da kuma inganta lafiyar jama’a.

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya za ta fara talllafawa da magani ga 'yan kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa Farfesa Pate ya bayyaana hakan ne yayin bikin kiwon lafiya da aka yi a birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta kashe bashin $232m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin sayen magani ga 'yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a fara sayen magunguna ta hanyar hadin-guiwa domin tabbatar da ana samun magagin da ake buƙata a kan farashi mai rahusa a asibitocin gwamnati.

Farfesa Pate ya ce wannan shiri zai taimaka wajen rage matsalolin rashin magunguna a asibitocin gwamnati tare da tabbatar da cewa kowa na iya samun kulawa ba tare da wahala ba.

Shirin inshora da tallafawa marasa galihu

Ministan lafiya ya ce gwamnatin Tinubu ta kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya da kashi 14 cikin ɗari a cikin shekarar 2024.

Gwamnati ta kafa asusun kudi na musamman domin tallafawa marasa galihu da kuma sauƙaƙa musu wajen lura da lafiyarsu.

Farfesa Pate ya ce gwamnatin ta kuma kafa cibiyoyin kula da cutar daji da wasu rashin lafiya da suka shafi mata.

Kara karanta wannan

An gano inda Tinubu ya 'tura' kudin da aka tara bayan cire tallafin man fetur

Maganar samar da kayan lafiya a Najeriya

Gwamnati ta ce ana shirin fara samar da magunguna da kayan aikin lafiya a cikin gida Najeriya domin rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.

Ana sa ran cewa idan hakan ya tabbata, za a samu sauki a kan abin da ya shafi sayen magani da sauran kayayyaki.

Gombe ta lashe gasar lafiya a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa jihar Gombe ta zama jiha mafi amfani da kirkira da fasaha a fannin kula da lafiya a jihohi 36 na Najeriya.

Bayan haka, jihar Gombe ta samu kyautar $400,000 bayan ta zama jiha ta biyu mafi kwarewa wajen kula da marasa lafiya a Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng