Bayan Hukuncin Kotu kan Rigimar Sarauta, Tsohon Minista ya Shiga Takarar Neman Rawani

Bayan Hukuncin Kotu kan Rigimar Sarauta, Tsohon Minista ya Shiga Takarar Neman Rawani

  • Bayan mutuwar marigayi Oba Gabriel Adekunle Aromolaran, tsohon Minista a Najeriya ya shiga jerin masu neman sarauta a jihar Osun
  • Farfesa Stephen Debo Adeyemi ya nuna kwadayinsa kan kujerar inda ya ce yana da kwarewa sosai a rayuwarsa
  • Hakan ya biyo bayan bude fagen neman sarautar Owa Obokun da ke yankin Ijesa a jihar Osun bayan mutuwar sarki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Takarar neman kujerar sarautar Owa Obokun ta fara daukar hankali a jihar Osun bayan mutuwar Oba Gabriel Adekunle.

Manyan mutane da dama ciki har da tsohon Minista a Najeriya sun fara nuna sha’awarsu domin gadon kujerar Owa Obokun.

Tsohon Minista ya shiga riguntsumin neman sarauta
Tsohon Minista, Stephen Debo Adeyemi ya shiga sahun masu neman kujerar sarauta a Osun. Hoto: Legit.
Asali: Original

Osun: Tsohon Minista ya fara neman sarauta

Tribune ta ce na baya-bayan nan da ya bayyana niyyarsa shi ne tsohon ministan lafiya a mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai suna Stephen Debo Adeyemi.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Stephen Debo kwararren likita ne ya bayyana kudurinsa na yi wa mutanen Ijesa hidima tare da jajircewa kan hadin kai da cigaba da kare al’adun gargajiya.

Adeyemi ya bayyana cewa yana shirye ya sadaukar da rayuwarsa don cigaban mutanen Ijesa, cewar The Guardian.

“Na yi wa kasata hidima a matsayin minista, na wakilci Najeriya a Canada, na yi fice a matsayin likitan tiyata."
"Kuma na shugabanci daya daga cikin manyan asibitocin kiwon lafiya a kasar, lokaci ya yi da zan yi wa mutanen Ijesa kai-tsaye hidima.”

- Farfesa Stephen Debo Adeyemi

Alkawuran da tsohon Minista ya yiwa al'umma

Farfesa Adeyemi ya kara jaddada muhimmancin hadin kai da zaman lafiya da hadin gwiwa tsakanin mutanen Ijesa.

Ya yi alkawarin aiki tare da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da ‘yan kasuwa domin amfana da dimbin albarkatun yankin.
“Idan muka yi aiki tare, za mu iya cin gajiyar albarkatun da Allah ya albarkace mu."

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan rikicin sarauta, ta hana gwamna naɗa sabon Sarki

- Farfesa Stephen Debo Adeyemi

Ana rigima kan binne tsohon sarki

Kun ji cewa rigima ta barke kan shirye-shiryen birne marigayi tsohon basarake a jihar Osun saboda zargin tatsar kudi.

Ana rigimar tsananin 'ya'yan marigayin, Oba Gabriel Adekunle na Ijesa da kuma kwamitin masarauta kan shirye-shiryen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.