Gombe Fa Fito ta 1 a Gasar Jihohin Najeriya 36, an ba Ta Kyautar Dubban Daloli

Gombe Fa Fito ta 1 a Gasar Jihohin Najeriya 36, an ba Ta Kyautar Dubban Daloli

  • Jihar Gombe ta zama jiha mafi amfani da kirkira da fasaha a fannin kula da lafiya a gasar da gwamnoni, UNICEF da NPHCDA suka shirya
  • A wani mataki na daban, jihar Gombe ta samu kyautar $400,000 bayan ta zama jiha ta biyu mafi kwarewa a yankin Arewa maso Gabas
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an samu nasarorin ne ta hanyar hadin gwiwar jama’a da ma’aikatan lafiya a jihar Gombe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe, Nigeria – Jihar Gombe ta ci gaba da kafa tarihi a fannin kiwon lafiya, ta zama jiha mafi kirkire-kirkire da aiki da fasaha a gasar kula da lafiyar farko ta 2023/2024.

An ruwaito cewa kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) tare da UNICEF da hukumar kula da lafiyar farko ta kasa (NPHCDA) ne suka shirya gasar.

Kara karanta wannan

Na farko a Arewa: Gwamna ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 1.5

Gombe
Jihar Gombe ta lashe gasar kiwon lafiya. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin bikin bayar da kyaututtuka, jihar Gombe ta samu kyautar sama da Naira miliyan 600 bayan ta zama ta biyu mafi kwarewa a fannin kula da lafiyar farko a Arewa maso Gabas.

Dalilin da ya sa jihar Gombe ta yi fice

Masu tantance jihohin sun bayyana cewa shirin tantance bayanai ta hanyar na’ura da sauran kirkire-kirkire da Gombe ta kawo a matsayin dalilin lashe gasar.

Ismaila Uba Misilli ya ce lashe gasar ya biyo bayan kokarin gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya na kawo sauye-sauye a fannin kiwon lafiya a jihar.

Tun a 2019 InuwaYahaya ya mayar da hankali kan gyara bangaren kiwon lafiya ta hanyar farfado da cibiyar kula da lafiyar farko guda daya mai aiki awanni 24 a mazabu 114 na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Kashim Shettima ya yabawa Gombe

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda Dr. Aliyu Modibbo Umar ya wakilta ya jinjinawa jihar Gombe da sauran jihohin da suka samu nasarori

Haka zalika, ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya jinjinawa wa Gombe saboda kirkire-kirkirenta a fannin lafiya.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya karbi kyaututtukan, ya sadaukar da su ga ma’aikatan lafiya da jama’ar Gombe, yana mai cewa:

"Waɗannan nasarori sun samo asali ne daga haɗin kan mu wajen tabbatar da an samu ingantaccen kulawar lafiya ga kowa da kowa."

- Gwamna Inuwa Yahaya

Gombe za ta kashe N28.9bn a gine gine

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da aikin ginin da zai ci lashe N28.9bn.

Legit ta ruwaito cewa gine-ginen da za a yi sun hada bangarorin zartarwa, majalisar dokoki da shari’a a wuri guda domin saukaka aikin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng