Rikici Ya Kunno Kai a Tsakanin Gwamnoni 36 kan Kudirin Harajin Tinubu
- Gwamnonin Najeriya sun kasa cimma matsaya kan kudirin harajin Bola Tinubu da aka aika ga majalisun tarayya
- Gwamnonin jihohi sun gudanar da taron da ya dauki awa 1 ba tare da fitar da sanarwa ko bayani ga manema labarai ba
- Hakan ya sanya ake hasashe kan rikici ya kunno a tsakaninsu kan amincewa da kudirin harajin shugaban kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Ana hasashen rikici ya barke tsakanin gwamnonin jihohin Najeriya 36 a karkashin kungiyar gwamnoni ta NGF kan kudirin haraji.
Kudirin haraji ya janyo ce-ce-ku-ce tare da fuskantar suka daga bangarori daban-daban tun lokacin da aka gabatar da shi.
Leadership ta wallafa cewa gwamnonin ba su cimma matsaya ba a taron da suka gudanar a ofishin NGF a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi jinkirin fara taron gwamnoni
Taron gwamnonin ya fara ne da karfe 10 na dare, amma wasu daga cikin gwamnonin ba su halarta ba a kan lokaci, lamarin da ya sanya aka fara tunanin cewa taron ba zai gudana ba.
Sai dai daga bisani, gwamnonin APC da suka hada kai sun iso tare da shugaban gwamnonin jam'iyyar, Sanata Hope Uzodimma.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa gwamnonin APC sun gana da shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje, kafin su isa taron.
Me ya janyo rikici a tsakanin gwamnoni
Babban batun da ke haddasa rikici shi ne yadda za a aiwatar da kudirin harajin, wadanda wasu gwamnonin ke ganin zai yi tasiri mara kyau ga jihohinsu.
Bayan kammala taron da misalin karfe 11 na dare, ba a samu sanarwa ko karin bayani daga shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ba.
Haka zalika ba a samu bayani daga shugaban gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodimma ba, wanda hakan ya kara tabbatar da cewa babu matsaya guda da aka cimma.
Tinubu ya gana da gwamnonin APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da gwamnonim jam'iyyar APC karkashin jagoranci gwamnan Imo.
Legit ta wallafa cewa Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ne kan wasu muhimman batutuwa da suka hada da maganar kudirin haraji.
Asali: Legit.ng