Na Farko a Arewa: Gwamna Ya Gabatar da Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 1.5

Na Farko a Arewa: Gwamna Ya Gabatar da Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 1.5

  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 1.5 ga majalisar dokokin jihar Neja
  • Rahotanni na nuni da cewa kasafin kudin ya mayar da hankali kan harkar noma da ci gaban tattalin arzikin jihar
  • Kasafin kudin jihar Neja ne mafi tsoka a Arewa yayin da jihar Legas ta gabatar da kasafin da ya haura Naira tiriliyan 3

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger – Gwamna Mohammed Umaru Bago ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2025 wanda adadinsa ya kai Naira tiriliyan 1.5 ga majalisar dokokin jihar Neja.

Gwamnan ya bayyana cewa sabon kasafin ya karu da kaso 48.3% fiye da na shekarar 2024 da ta gabata.

Gwamna Bago
Gwamnan Neja ya gabatar da kasafin kudin n1.5tn. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan, Ibrahim Balogi ya wallafa a Facebook cewa kasafin ya mayar da hankali kan bunkasar harkar noma, inganta bangarorin tsaro, lafiya, ilimi, ruwa, da tsaftar muhalli.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno kai a tsakanin gwamnonin jihohi 36 kan kudirin harajin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman abubuwa a kasafin kudin Neja

Gwamna Bago ya bayyana cewa bangaren gine-gine da sabunta birane shi ne ya samu kaso mafi tsoka na kasafin, inda aka ware masa Naira biliyan 437.

Haka zalika gwamna Umaru bago ya bayyana cewa bangaren shari'a ya samu kaso mafi kankanta na Naira biliyan 3.5

"Wannan kasafi zai mayar da hankali kan tsaron rayuka da dukiyoyi, noma da samar da abinci, lafiya, ilimi, da ci gaban abubuwan more rayuwa."

- Gwamna Umaru Bago

Gwamna Bago ya yabawa majalisar dokokin Neja

Rahoton Channels Televison ya nuna cewa gwamna Bago ya yabawa majalisar dokokin jihar kan hadin kai da goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da nasarar kasafin.

A jawabinsa, kakakin majalisar dokokin Neja, AbdulMalik Sarkin Daji, ya yaba wa gwamnan bisa irin dabarun tafiyar da kudaden jihar.

Gabatar da kasafin ya samu halartar mataimakin gwamna, Yakubu Garba; matar gwamna, Hajiya Fatima Umaru Bago; sarakunan gargajiya, manyan malamai da jami’an gwamnati.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta kashe bashin $232m

An gabatar da kasafin N3tn a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna jihar Legas, Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin 2025 ga majalisar dokoki.

Legit ta rahoto cewa gwamna Sanwo-Olu ya gabatar da sama da Naira tiriliyan 3 a matsayin kasafin kudi domin gudanar da muhimman ayyuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng