'Ya Yi Kokari a Mulkinsa': Basarake Ya Fadi Dalilin Kai Wa Buhari Ziyara a Gidansa

'Ya Yi Kokari a Mulkinsa': Basarake Ya Fadi Dalilin Kai Wa Buhari Ziyara a Gidansa

  • Fitaccen basarake a Kudancin Najeriya ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Katsina
  • Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yabawa tsohon shugaban kasar lokacin da yake mulkin Najeriya
  • Basaraken ya ce abin mamaki Buhari ya kara murmurewa kaman wani matashi duk da shekarun da yake da shi a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yabawa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Basaraken ya yabawa Buhari bisa kokarinsa yayin mulkinsa a matsayin shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023.

Basarake ya fadi dalilin ziyartar Buhari a gidansa
Ooni na Ife ya yabawa salon mulkin Muhammadu Buhari a Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Basarake ya sha mamaki da ganin Buhari

Ooni na Ife ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya aikewa Punch bayan ziyararsa ga Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce wannan ziyara ta ba da dama mai muhimmanci don tattaunawa tsakanin basaraken da Buhari kan muhimman batutuwan da suka shafi cigaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda babban sarkin Yarabawa ya kai wa Buhari ziyarar ban girma a Daura

Yayin da yake nuna farin cikinsa, Oba Ogunwusi ya lura cewa Buhari ya bayyana cikin kyakkyawar walwala da kuzari a lokacin haduwarsu.

“Yanzu haka ya zama kamar an rage masa shekaru 30."
“Zan iya fadawa dukkan Najeriya cikin farin ciki cewa yana rayuwa cikin koshin lafiya sosai."
"Idan ka gan shi, za ka yi mamakin yadda yake cikin nutsuwa da kuzari, yana cike da walwala."
"Yana nan kaman wani matashi da bai kai shekarunsa ba kuma Allah ya albarkace shi da sabon lafiya.”

- Oba Adeyeye Ogunwusi

Ooni na Ife ya yaba salon mulkin Buhari

Basaraken ya jinjinawa ƙoƙarin Buhari yayin shugabancinsa, yana cewa:

“Ya yi duk mai yiwuwa a matsayinsa na shugaban Najeriya wajen jagorantar ƙasar kan hanya madaidaiciya.”
“Wannan taron ba kawai wata ziyara ta sada zumunci ba ce, amma wani muhimmin mataki ne na diflomasiyya da ke nuna muhimmancin tattaunawa tsakanin shugabanni a faɗin ƙasa."

Kara karanta wannan

'Laifin Buhari ne': Lauya ya kare Tinubu kan fifita ƙabilar Yarbawa a gwamnatinsa

- Oba Adeyeye Ogunwusi

Ooni na Ife ya kai wa Buhari ziyara

A baya, kun ji cewa Mai Martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura.

Rahotanni sun nuna cewa Oba Adeyeye Ogunwusi ya kuma ziyarci fadar sarkin Daura tare da Buhari kafin barin garin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.