Akwai Matsala: Bankuna Sun Rage Yawan Kuɗin da Jama'a Za Su Riƙa Cirewa Kullum
- A jihar Nasarawa, an rage yawan kudin da mutane za su iya cirewa a cikin bankuna zuwa N10,000, sai N20,000 a na'u'rorin ATM
- Ma’aikatan bankuna sun danganta matsalar da karancin kudi, inda masu POS ke caji mai tsada, suna karbar N200 kan N5,00
- Jama’a na cikin matsala yayin da wannan tsarin cire kudi ya takura musu, suna kira ga gwamnati da ta kawo dauki a lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Bankuna a jihar Nasarawa sun rage yawan kudin da abokan huldarsu za su iya cirewa a cikin banki zuwa N10,000.
Duk da haka, ba su rage ka'idar N20,000 da abokan hulda ke iya cirewa daga na'urar ATM a kullum ba, wanda ya jawo wahalar samun kudi ta karu.
Bankuna sun sanya dokar cire kudi
A bankuna da ke Mararaba, Karu, mutane sun nuna damuwa sosai kan matakin da bankunan suka dauka na rage kudin da za a cire, a cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu abokan huldar bankunan sun nuna rashin amincewarsu tun a cikin bankuna, suna masu korafi kan yadda rage kudin da za su cire zai kawo musu matsaloli.
Ma’aikatan bankuna da jaridar ta tattauna da su, sun nuna cewa matsalar ta samo asali ne daga karancin takardun kudin a cikin ma'ajiyar kudin bankunan.
Bankuna sun fadi matsalar da aka samu
Wani ma’aikacin banki ya ce:
“Ba mu da isasshen kudi. Muna dai raba abin da muke da shi nega abokan huldar mu."
Wannan matsalar ta shafi bankuna da dama a yankin da aka ziyarta, inda ake ganin abokan huldar suna fuskantar karancin kudin.
Wasu kuma na ganin cewa an samu karancin kudin ne sakamakon watan Disamba da ake ciki, inda aka saba ganin karancin kudi saboda bukukuwan Kirsimeti.
Koma dai ya ne, karancin kudin ya bude kofa ga masu sana'ar POS, inda suka tsawwala kudin da suke cajar abokan huldarsu wajen cire kudi.
Masu POS sun tsawwala kudin caji
A yanzu farashin cire kudi daga POS ya karu sosai. Ana caji tsakanin N200 zuwa N250 a kan N5,000, sannan ana karbar N400 domin a cire N10,000.
Karin kudin bai tsaya a nan ba, an ce masu sana'ar POS na karbar N800 idan za su ba da N20,000, yayin da masu neman N40,000 za su biya cajin N1,600.
Wannan lamari ya jefa jama'a cikin mawuyacin hali, musamman ga wadanda ke bukatar kudi domin biyan wata bukata ta gaggawa.
Tuni dai aka fara yin kiraye kiraye ga gwamnati da ta dauki mataki na wadatar da takardun kudi a kasar domin rage wahalhalun da suke damun jama'a.
An fara karancin kudi a jihar Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa an fara fuskantar matsalar karancin kudi a Kano wadda take neman zama barazana ga harkokin kasuwanci a jihar.
Karancin takardun Naira dai ba iya ga mazauna jihar Kano ya shafa ba, har masu sana'ar POS bai kyale ba, wadanda suka ce suna shan wahala kafin su samu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng