'Za a Tsige Ku': Gwamnatin Tinubu Ta Gargadi Gwamnoni kan Kudin Kananan Hukumomi

'Za a Tsige Ku': Gwamnatin Tinubu Ta Gargadi Gwamnoni kan Kudin Kananan Hukumomi

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana hukuncin da gwamnoni za su fuskanta kan katsalandan da kudin kananan hukumomi
  • Babban lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan shari'a na kasa, Lateef Fagbemi SAN shi ya yi wannan gargadi
  • Fagbemi ya ce duk gwamnan da ya taba kudin kananan hukumomi zai iya fuskantar tsigewa daga mukaminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi ya gargadi gwamnonin jihohi kan kudin kananan hukumomi.

Lateef Fagbemi ya ce duk gwamna da ya yi katsalandan ga kudin kananan hukumomi zai fuskanci tuhumar aikata laifi wanda ka iya kaiwa ga tsigewa.

Gwamnatin Tinubu ta gargadi gwamnoni kan kudin kananan hukumomi
Gwamnatin Bola Tinubu ta gargadi gwamnoni kan katsalandan da kudin kananan hukumomi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen gwamnoni

Tribune ta ce Fagbemi ya fadi haka ne yayin taron shekara-shekara na Kungiyar 'Yan Jarida Masu Ruwaito Al’amuran Shari’a (NAJUC), reshen Abuja.

Kara karanta wannan

Abba ya sauke sakataren gwamnati, Baffa Bichi, Sagagi da kwamishinoni 5 a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fagbemi ya kuma gargadi shugabannin kananan hukumomi 774 a Najeriya kan almubazzaranci da kudadensu.

A cikin sanarwar, Fagbemi ya bayyana tasirin ƙananan hukumomi da irin samar da cigaba da suke yi a kasa, cewar The Nation.

“Hukuncin Kotun Koli na ranar 11 ga Yulin 2024, ya ba kananan hukumomi ‘yancin kuɗaɗensu."
"Duk wani gwamna da ya yi katsalandan ga kudaden kananan hukumomin jiharsa, zai kasance ya aikata babban laifi, wanda ka iya kaiwa ga tsigewa.”

- Lateef Fagbemi

Gwamnatin Tinubu ta ba kananan hukumomi shawara

Lateef Fagbemi ya shawarci shugabannin kananan hukumomi da sauran jami’ai su mayar da hankali kan aikinsu na kundin tsarin mulki.

“Dole a tabbatar da cewa kowane yaro yana samun ilimin firamare, mata masu juna biyu da jarirai sun samu kulawar lafiya mai inganci."
"Sannan mabukata a cikin al’umma su amfana daga shirye-shiryen tallafi masu dorewa."

- Lateef Fagbemi

Kotu ta zauna kan batun kudin kananan hukumomi

Kara karanta wannan

NLC ta matsawa gwamna, ya amince N80,000 ya zama sabon mafi ƙarancin albashi

Kun ji cewa Babbar Kotun jihar Kano ta tsaida lokacin yin hukunci kan korafin da aka shigar game da kudin kananan hukumomi.

Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) ta shigar da karar CBN da wasu kan neman hana kananan hukumomin hakkinsu.

Daga cikin wadanda ake kara akwai Ministan shari'a da hukumar RMAFC da wasu bankunan 'yan kasuwa da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.