"Ko Sama da Ƙasa Za Su Haɗe": Wike Zai Ci gaba da Rusa Gine Ginen Mutane a Abuja

"Ko Sama da Ƙasa Za Su Haɗe": Wike Zai Ci gaba da Rusa Gine Ginen Mutane a Abuja

  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin cigaba da rusa gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba a Abuja
  • Nyesom Wike ya gargadi masu karbar filaye ba tare da izini ba da cewa ba za su tsallake hukunci ba, komai matsayin su
  • Ministan ya kuma umarci masu biyan haraji da su gaggauta biya ko kuma a kwace filayen su domin rabawa masu bin doka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi alkawarin cigaba da rusa gidajen mutane da aka gina ba bisa ka’ida ba a filayen gwamnati.

Rahotanni sun bayyana cewa Wike na ci gaba da fuskantar suka kan rusa gine gine ba tare da bincike da gabatar da cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

An gano inda Tinubu ya 'tura' kudin da aka tara bayan cire tallafin man fetur

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan ci gaba da rusau
Wike ya sha alwashin ci gaba da rusau a Abuja. Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Abuja: Wike zai ci gaba da yin rusau

Yayin rabon motoci ga hukumomin tsaro a Abuja, Wike ya bayyana cewa ba zai bari barazana ta dakatar da shi daga rusau ba, a cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce gidajen da ake rusa wa an gina su ne ba bisa ka’ida ba, wasu kuma suna haifar da barazanar tsaro ga mazauna Abuja.

Wike ya dage cewa babu ja da baya, ya kuma yi alkawarin rusa gidajen da aka gina da shantunan da suka saba doka.

Wike ya lashi takobin kare dokar fili

Yayin da ya ce babu wata gwamnati da za ta zura ido ana amafani da filaye ba bisa doka ba, Wike ya ce:

"Zamu tabbatar babu wanda zai sake yin amfani da filin gwamnati ba tare da izini ba. Mun dauki mataki mai tsauri
"Ka gina gida a filin da ba a bayar da shi bisa ka’ida ba? To kada ka yi tunanin za mu sassauta maka, za mu rusa shi ko sama za ta fado."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

Wike ya gargadi masu filaye a Abuja

Channels TV ya rahoto Wike ya gargadi masu biyan haraji kan filaye cewa idan ba su biya ba, za a kwace filayen kuma a sake raba su ga wadanda za su iya biya.

Ministan babban birnin tarayyar ya yi barazanar cewa duk wanda ya yi wasa da biyan haraji a kan lokaci, zai rasa filinsa ba tare da jinkiri ba.

Ya umarci hukumomin tsaro da su yi amfani da motocin da ya raba masu domin tabbatar da tsaro, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Majalisar dattawa za ta binciki Wike

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta ba da umarnin gudanar da bincike kan gine ginen da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike yake rusawa.

Majalisar ta kafa wani sabon kwamiti da zai binciki rusau ɗin ministan Abujan yake yi wanda ya jawo mutane da dama suka rasa muhallinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.