Ana Tsaka da Batun Kudirin Haraji, Mataimakin Shugaban Kasa Ya Shiga Taron NEC a Abuja
- Sanata Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki ta kasa watau NEC a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja
- Taron wanda aka saba yi a wata-wata ya samu halartat gwamnoni, ministoci da hukumomin gwamnati da ke cikin majalisar
- Ana sa ran taron zai tattauna kan batun ƴan sandan jihohi kuma da yiwuwar majalisar NEC ta faɗi matsayarta a wannan karon
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa (NEC) karo na 146 a Aso Rock.
Gwamnonin jihohin Najeriya, ministoci da wakilan hukumomin da ke cikin NEC sun halarci zaman na yau Alhamis, 12 ga watan Disambar 2024.
Abin da ake tattaunawa a taron NEC
The Nation ta tattaro cewa taron Majalisar tattalin arziki da aka saba yi a kowane wata, ya kan tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara taron ne bayan isowar mataimakin shugaban kasa a ɗakin taron da ke Aso Rock da misalin ƙarfe 12:06 na tsakar rana, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wannan taron, ana sa ran ƴan majalisar tattalin arzikin za su tattauna kan batun ƴan sandan jihohi, kasafin kuɗin 2025 da wasu batutuwa da da suka taso.
NEC za ta faɗi matsaya kan yan sandan jihohi
Idan baku manta ba a taron da ya gabata, NEC ta bai wa wasu jihohi uku wa'adin mako guda su mika rahoto da matsayarsu kan ƴan sandan jihohi da ake shirin kirƙirowa.
NEC ta kuma faɗi ra'ayinta kan sabon kudirin sauya fasalin harajin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar a Majalisa, ta bukaci ya janye domin ƙara tattaunnawa.
A wannan zaman na yau Alhamis, ana tsammanin majalisar tattalin arziki za ta duba rahoto kan batun kirkiro ƴan sandan jihohi kuma ta sanar da matsayarta.
Tattalin arzikin Najeriya ya farfaɗo
Ku na da labarin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce abubuwa su na kyau matuka, ganin cewa tattalin arziki ya fara dawowa hayyacinsa.
Kashim Shettima ya fadi haka ne lokacin da ya ja tawagar gwamnatin tarraya zuwa bude kasuwar duniya da ke Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng