Shugaba Tinubu Ya Gana da Wasu Gwamnoni Ana Tsaka da Surutu kan Kudirin Haraji
- Mai girma shugaban kasa ya gana da gwamnonim jam'iyyar APC karkashin jagoranci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma
- Bola Tinubu ya gana da gwamnoni ne kan wasu muhimman batutuwa ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, 2024
- Wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta surutu kan sabon kudirin sauya fasalin haraji da ke gaban Majalisa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Shugaba Tiinubu ya gana da gwamnonin ne kan wasu muhimman batutuwa a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ne ya tabbatar da hakan a wani gajeren sako da ya wallafa a shafin X yau Alhamis da safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ganawar Tinubu da gwamnonin APC
Sai dai hadimin shugaban ƙasar bai bayyana ajendar da shugabannin suka tattauna ba wannan zama ba.
Duk da ba a faɗi abin da suka tattauna ba ana ganin taron ba zai rasa alaƙa da kudirin sauya fasalin haraji wanda ke gaban majalisar tarayya ba.
Kudirin dai na ci gaba da shan suka daga ɓangarori daban-daban musamman Arewacin Najeriya.
Har ila yau kudirin ya raba kawunan ƴan majalisar tarayya, inda wasu ke goyon bsya wasu kuma ke ganin a sake nazari kan wasu tanade-tanaden da ke ciki.
Bugu da ƙaru, mun kawo maku rahoton cewa gwamnoni akalla 15 sun gana a Abuja jiya Laraba da daddare kan batun kudirin.
Abin da aka tattaunawa a taron
Yanzu kuma fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Aso Villa.
"A jiya Shugaba Tinubu ya gana da ƴan kungiyar gwamnonin APC karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, inda suka tattauna muhimman batutuwa."
- Dada Olusegun.
Bola Tinubu ya naɗa sabon Akanta-Janar
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da nadin sabon mukaddashin Akanta-janar na Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi a matsayin Akanta-janar na Tarayya a ranar Talata 10 ga watan Disambar 2024.
Asali: Legit.ng