Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna, Sun Tura Miyagu Zuwa Barzahu

Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna, Sun Tura Miyagu Zuwa Barzahu

  • Ƴan bindiga sun kai hari a wata rugar Fulani da ke jihar Kaduna inda suka sace shanu masu yawa bayan sun firgita Makiyaya
  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi wa ƴan bindigan kwanton ɓauna inda suka samu nasarar hallaka guda uku daga cikinsu
  • Sojojin sun kuma ƙwato shanun da ƴan bindiga suka sace a rufar Fulanin da ke ƙauyen Kurutu na ƙaramar hukumar Kachia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sojoji sun sun harbe ƴan bindiga uku bayan sun yi musu kwanton ɓauna a jihar Kaduna.

Wasu makiyaya biyu sun jikkata bayan an ƙwato shanun da ƴan bindigan suka sace a ƙauyen Kurutu da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a jihar Kaduna Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ce wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Kwaɗayin mulki": An faɗi wasu manyan ƴan siyasa a Arewa da ke taimakawa ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an gano shanun da tumaki ne a ranar Asabar a dajin Hayin-Dam, wanda a cewarsa yana iyaka da ƙauyen Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko.

Shugaban al'ummar ya ce ƴan bindigan sun kai farmaki wata rugar Fulani a ƙauyen Kurutu inda suka yi awon gaba da wasu shanu tare da raunata wasu makiyaya guda biyu.

Ya ce ƴan bindigan da isar su rugar, sun yi ta harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa makiyayan guduwa, kafin daga nan su kwashe shanun.

Sojoji sun yi wa ƴan bindiga ƙwanton ɓauna

"Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 4:23 na Asuba, ƴan bindigan suka mamaye rugar Fulanin, amma cikin ikon Allah, an sanar da wasu sojoji dake dawowa daga shingen bincikensu na Bishini."
"Bayan samun labarin sai suka yi musu kwanton ɓauna. Sun kashe uku daga cikin ƴan bindigan tare da ƙwato shanun."

- Wani shugaban al'umma

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun samu nasarori a Kaduna

Ya ce sojojin sun kai makiyayan biyu da suka jikkata zuwa asibiti a ƙauyen Katari da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Sojoji sun fafata da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar 'Operation Golden Peace' ta kai farmaki kan ƴan bindiga a jihar Benue.

Farmakin da sojojin suka kai ya maida hankali ne kan fatattakar ƴan bindiga da suka addabi yankunan Akahagu da China a karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng