An Gano Inda Tinubu Ya 'Tura' Kudin da aka Tara Bayan Cire Tallafin Fetur
- Ministan yada labarai ya bayyana cewa kudin da aka adana daga cire tallafin mai ana amfani da su wajen muhimman ayyuka
- Mohammed Idris ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ta mayar da hankali kan samar da motocin CNG domin saukake harkar sufuri
- Ministan ya ce Bola Tinubu yana da nufin farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da rage wa talakawa nauyin haraji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu ke amfani da kudin da aka adana daga cire tallafin mai.
Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na amfani da kudin wajen aiwatar da ayyuka masu amfani ga ‘yan Najeriya.
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa a Facebook cewa Mohammad Idris ya yi jawabin ne yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin noma da kawo motocin CNG
Ministan ya ce cire tallafin man fetur ya kawo ci gaba wajen ba manoma tallafi domin samar da wadataccen abinci a Najeriya.
Haka zalika ya bayyana cewa an yi amfani da kudin wajen samar da motocin gas na CNG wanda ke rage kudin sufuri da kashi 60%.
Tallafin karatun dalibai da habaka ilimi
Mohammaed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kafa dokar ba dalibai lamuni domin bai wa matasa damar samun ilimi mai dorewa.
The Nation ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce ana amfani da kudin da aka tara daga cire tallafin mai ne wajen ba matasa tallafin karatn NELFund
Haka zalika ana amfani da kudin wajen ba talakawa rance mai sauki domin bunkasa sana'o'i da habaka tattali.
Maganar minista kan kudirin haraji
Mohammaed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana kan turbar farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar sabunta tsarin haraji domin saukakawa talakawa.
Ya kara da cewa Bola tinubu ya mai da hankali kan bunkasa ababen more rayuwa, inganta rayuwar ‘yan Najeriya, da samar da tattalin arziki mai dorewa.
An radawa cibiya sunan Tinubu a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar shige da fice ta Najeriya ta sanya sunan shugaba Bola Ahmed Tinubu a cibiyarta ta fasahar zamani.
Shugabar hukumar NIS, Kemi Nanna Nandap ta ce cibiyar za ta taimaka wajen kula da shige da fice tare da kare iyakokin Najeriya.
Asali: Legit.ng