Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Ya Naɗa Muƙamai Sama da 20 a Ɓangarori 3
- Gwamnatin Kano ta yi sababbin naɗe-naɗe a muhimman guraben tafiyar da al'amura a jihar
- An yi naɗin a ɓangarorin shari'a, zakka da hubusi da kuma hukumar ma'aikatan jihar Kano
- Gwamnati ta shawarci sababbin ma'aikatan da su tabbatar sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya naɗa muhimman muƙamai aƙalla 13 a ɓangarorin ma'aikata, shari'a da hukumar zakka da hubsi.
Gwamnatin ta bayyana cewa an yi naɗe-naɗen ne bisa tsarin doka, kamar yadda aka sahalewa gwamnan jihar ya aiwatar.
A sakon da darakta janar ga gwamnan a kan yaɗa labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook, an naɗa mukamai aƙalla 23 a ɓangarori daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naɗe-naɗen gwamna Abba a ɓangaren ma'aikata
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa mutane uku muƙamai a hukumar ma'aikatan gwamnatin jihar Kano.
Mutanen da aka naɗa sun haɗa da;
1. Injiniy Ahmad Ishaq – Shugaban hukuma Alhaji Abdullahi Mahmoud – Babban memba I Ado Ahmed Mohammed – Babban memba II
Shari'a: Gwamna Abba ya naɗa mutum 10
Mutane 10 da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya naɗa mukamai a hukumar shari'a ta jihar sun haɗa da;
Sheikh Abbas Abubakar Daneji – Shugaban hukuma Malam Hadi Gwani Dahiru – Kwamishina na I Sheikh Ali Dan’Abba – Kwamishina na II Malam Adamu Ibrahim – Memba Malam Abubakar Ibrahim Mai Ashafa – Memba Malam Naziru Saminu Dorayi – Memba Sheikh Kawu Aliyu Harazumi – Memba Sheikh Mukhtar Mama – Memba Sheikh Ibrahim Inuwa Limamin Ja’en – Memba Sheikh Dr. Sani Ashir – Sakataren Hukuma/Memba
Hukumar Zakka: Abba Gida Gida ya yi naɗi
A hukumar zakka da hubsi ma, gwamnatin Kano ta naɗa mutane 10 muƙaman da su ka haɗa da Barista Habibu Dan Almajiri a matsayin shugaban hukumar, Sheikh Nafiu Umar Harazumi, kwamishina na I. An naɗa Dr. Ali Quraish kwamishina II, Abdullahi Sarkin Sharifai a memba, Adamu Muhammad Andawo memba. Sauran sun haɗa da Yahaya Muhammad Kwana Hudu memba, Sheikh Hassan Sani Kafinga memba, Sheikh Arabi Tudun-Nufawa memba, Sani Shariff Umar Bichi memba da kuma gurbin muƙamin sakatare.
Abba Gida Gida zai biya kudin makaranta
A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ɗauki alkawarin ceto shaidar kammala karatun ɗaliban jihar da aka kai karatu kasar Cyprus a zamanin Abdullahi Ganduje.
Gwamnan ne da kansa ya ziyarci Cyprus domin tattaunawa da hukumomin jami'ar da daliban su ka kammala karatu da summary a cimma matsaya don sakin shaidar karatun.
Asali: Legit.ng