Wutar Lantarki: Gwamnati Ta Fadi Shirinta da Jamus bayan Shiga Duhu Karo na 12 a 2024
- Gwamnatin tarayya ta ce akwai shirin da ta ke da shi da zai inganta wutar lantarki a faɗin ƙasar nan
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya fadi shirin a ranar Laraba bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- Haka kuma jawabi na so ya zo a dai-dai lokacin da Najeriya ta faɗa a cikin duhu karo na 12 a shekarar nan da za ta kare a cikin kwanaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Ministan makamashi na kasa, Adebayo Adelabu ya shaida wa jama'a cewa akwai shirin da zai kara habaka wadatuwar hasken wutar lantarki. Mista Adelabu ya yi wannan bayani ne a lokacin da ƴan kasa su ka ƙara tsunduma a cikin duhu a karo na 12 a 2024.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ministan makamashi, Adelabu ya tabbatar da cewa akwai wani shiri da kamfani a kasar Jamus da zai inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.
Shirin Najeriya da Jamus a kan wutar lantarki
Jaridar Punch ta wallafa cewa ƙasar nan na shirin karo megawat 150 na hasken wutar lantarkin da ƴan Najeriya ke sha domin wadata jama'a da hasken.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan ƙarin zai samu ne sakamakon kammala matakin gwaji na shirin wutar lantarki na shugaban ƙasa (PPI) da aka fara da haɗin gwiwar Siemens na Jamus.
Shirin gwamnati a kan wutar lantarki
Mista Adebayo Adelabu, Ministan da ke kula da harkokin makamashi ya ce akwai dangantaka mai ƙwari tsakanin ƙasar nan da Jamus tun bayan wata yarjejeniya ta shekarar 2023.
Daga cikin shirin, akwai shigo da kuma girka transfoma 10 na wutar lantarki tare da tashoshin rarraba wuta guda 10, Kuma har an kammala guda takwas daga ciki.
Wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa
A wani labarin, kun ji cewa kamfanoni rarraba hasken wutar lantarki a Najeriya sun hasken wuta da za su raba ga abokan hulɗarsu saboda durƙushewar tashar wuta.
Jama'a da dama sun shiga duhu bayan lalacewar wutar lantarkin karo na 12 a shekarar 2024, yayin da ayyuka su ka tsaya cak, inda kamfanin rarraba wuta ya ba jama'a haƙuri.
Asali: Legit.ng