Yan Sanda, Sarakuna da Mutanen Gari Sun Hadu domin Murkushe 'Yan Daba a Kano

Yan Sanda, Sarakuna da Mutanen Gari Sun Hadu domin Murkushe 'Yan Daba a Kano

  • An shirya taron masu ruwa da tsaki a Kano domin tattauna hanyoyin dakile rikice-rikicen daba a tsakanin matasa a yankunan jihar
  • Masu unguwanni, dattijai, da kwamitocin tsaro sun yarda da yin aiki tare da 'yan sanda wajen gano masu haddasa rikice-rikicen
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi alkawarin ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar kano -A ranar 11 ga Disamba, 2024, aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a hedkwatar rundunar ‘yan sandan Kano domin samo hanyar murkushe 'yan daba.

Taron ya samu halartar shugabannin unguwanni, dattijai, da mambobin kwamitocin tsaro daga yankunan Kofar Mata, Zango, Zage, Yakasai A, Yakasai B, Fagge da wasu unguwannin Kano.

Kara karanta wannan

An kama rikakken 'dan bindiga mai raba makamai a jihohin Arewa

Yan sanda
An yi taro domin shawo kan 'yan daba a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Kakakin 'yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa an cimma matsaya kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da tsaro jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarjejeniyoyin da aka cimma a taron

Masu ruwa da tsaki sun cimma yarjejeniyoyi kamar haka:

1. Hadin gwiwa da 'yan sanda

An yarda a rika ba da bayanai masu muhimmanci domin dakile rikice-rikice da gano wadanda ke da hannu a aikata laifuffukan daba.

2. Tallafawa ayyukan 'yan sanda

Daga cikin abubuwan da aka cimma akwai jaddada goyon bayan jama’a wajen ba da bayanai da kuma taimakawa wajen cafke masu laifi.

3. Rika shirya zama kan tsaro

An amince a rika gudanar da tarurruka na tsaro domin tattauna matsaloli da shirya dabarun tabbatar da zaman lafiya.

Bayanin kwamishinan 'yan sanda

A madadin Kwamishinan 'yan sanda, ACP Abdulkarim Abdullahi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen cafkewa da gurfanar da masu jagorantar rikice-rikicen daba a gaban shari’a.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

ACP Abdullahi ya ce suna godewa gwamnatin Kano da duk masu ruwa da tsaki kan goyon bayan da suke ba su domin tabbatar da tsaro a jihar.

Kwamishinan ya kuma roki jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai tare da yin kira ga matasa su guji aikata duk wani abu da zai janyo tashin hankali.

Za a cafke 'yan daba a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kai ziyara unguwanni da dama domin magance matsalar 'yan daba.

Kwamishinan 'yan sanda, CP Salman Dogo Garban ba da umarnin kama duk masu hannu wajen tayar da fadan daba da ake yi wasu unguwannin jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng