Wasu Gwamnoni 15 Sun Shiga Taro a Abuja kan Kudirin Harajin Bola Tinubu
- Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta shiga taro na musamman a Abuja kan kudirin harajin Bola Tinubu da ke gaban majalisa
- An ruwaito cewa galibin gwamnonin da suka halarci zaman ƴan APC ne sai guda biyu kaɗai ƴan jam'iyyun adawa
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da kudirin haraji ke ci gaba da kawo cece-kuce tsakanin manyan Najeriya ciki har da gwamnoni
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF sun shiga wani taro a sakatariyar kungiyar da ke Abuja a daren Laraba.
Gwamnoni 15 galibi ƴan jam'iyyar APC mai mulki ne aka gani sun shiga wurin taron zuwa yanzu da muke haɗa maku wannan taron.
Gwamnoni sun shiga ganawa a Abuja
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, gwamnoni biyu kaɗai aka hanga na jam'iyyun adawa sun halarci taron NGF a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan tsagin adawar da aka gani sun shiga taron su ne gwamnan jihar Abia, Alex Otti na jam'iyyar LP da takwaransa na jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo na APGA.
Ba a bayyana ajandar taron ga manema labarai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ranar Laraba da daddare, Ripples Nigeria ta kawo.
Dalilin taron gwamnonin Najeriya
Sai dai ana ganin taron gwamnonin ba zai rasa alaƙa da kudirin harajin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba, wanda ke ci gaba da shan suka.
Kudirin wanda ke gaban Majalisar Tarayya na ci gaba da shan suka daga gwamnonin musamman ƴan Arewa, waɗanda ke ganin ba a yi ma yankinsu adalci ba.
Gwamnoni 19 na jihohin Arewacin Najeriya sun yi watsi da wasu sashe na kudirorin, inda suka bukaci shugaban ƙasar ya janye ya ba da damar sake tattaunawa.
Ana ganin dai wannan kudiri na haraji da wasu muhimman batutuwa ne gwamnonin za su tattauna a wannan zama da ke gudana a Abuja.
Yadda kudirin harajin Tinubu ya raba kawuna
A wani rahoton, kun ji cewa har yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan kudurin haraji da aka gabatar a gaban majalisar Najeriya.
Rahoto ya bayyana kadan daga abin da kudurin ya kunsa da kuma abin da wasu manyan Najeriya suka hango game da kudurin.
Asali: Legit.ng