Tushen Wutar Najeriya Ya Lalace, Al'umma Sun Shiga cikin Duhu a Ko Ina

Tushen Wutar Najeriya Ya Lalace, Al'umma Sun Shiga cikin Duhu a Ko Ina

  • Najeriya ta sake fadawa cikin duhu yayin da aka rahoto cewa tashar wutar lantarki ta durkushe a ranar Laraba, 11 ga Disamba
  • An rahoto cewa tashar wutar ta durkushe ne da misalin karfe 1:33 na rana, kamfanonin lantarki sun rasa wutar rabawa jama'a
  • Durkushewar da tashar wutar ta yi a yau Laraba dai shi ne akalla karo na 12 a 2024, kuma ya jawo tsayawar ayyuka a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Al'ummar Najeriya sun shiga cikin duhu a sanadiyyar lalacewar tushen wutar lantarki na kasa kamar yadda rahotanni suka nuna.

Lantarki
Tsuhen wuta ya lalace a Najeriya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Rahotanni daga shafin yanar gizon ISO me alaka da kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), sun nuna cewa babu wata tashar samar da wuta da ke aiki tun karfe 2:00 na rana.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta ayyana kujerar gwamna a matsayin babu kowa a kai

Legit ta tabbatar da lalacewar tushen wutar ne a cikin wani sako da kamfanin rarraba wuta na JED ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin JED kan lalacewar lantarki

Kamfanin JED ya tabbatar da cewa dukkanin jihohin da ke ƙarƙashin ikon sa sun rasa wutar lantarki sakamakon rushewar tushen wuta na kasa.

Shugaban sashen hulɗa da jama’a na kamfanin, Dr Friday Adakole Elijah, ya bayyana cewa rashin wutar ya faru ne da misalin karfe 1:33 na rana a yau, Laraba.

JED ya nemi afuwar abokon hulda

Kamfanin JED ya nemi abokan cinikinsa su yi haƙuri tare da fahimtar matsalar, yana mai cewa ana aiki tukuru domin tabbatar da dawo da wuta cikin gaggawa.

Daily Trust ta wallafa cewa Dr. Elijah ya kara da cewa suna godiya kan haƙuri da goyon bayan jama'a a irin wannan lokacin.

Rushewar tushen wuta na ci gaba da zama babban kalubale ga Najeriya, wanda ke shafar tattalin arziki da rayuwar jama’a kai tsaye.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwa, kayayyakin miliyoyin naira sun kone

Najeriya za ta ranto $500m saboda lantarki

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar tarayya ta amincewa gwamnatin Bola Tinubu ta ranto $500m domin sanya na'urar auna shan wuta.

Hukumar da ke lura da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ce za ta mikawa makudan kudin domin ta tabbatar da an sayo mitar da za a rarraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng