Majalisa Ta Ayyana Kujerar Mataimakin Gwamna a Matsayin Wanda Babu Kowa a Kai
- Kujerar Dennis Idahosa mai wakiltar mazaɓar Ovia daga jihar Edo ta zama wacce babu kowa a kanta daga ranar Laraba, 11 ga watan Disamban 2024
- Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya ayyana kujerar mataimakin gwamnan na Edo a matsayin hakan a ranar Laraba
- Ayyana kujerar ta sa ta majalisar a matsayin wacce babu kowa a kanta na zuwa ne bayan ya zama mataimakin gwamnan jihar Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ayyana kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo, Dennis Idahosa, a matsayin wacce babu kowa a kanta.
Abbas Tajudeen ya ayyana kujerar Dennis Idahosa mai wakiltar mazaɓar Ovia daga jihar Edo, a matsayin wacce babu kowa a kanta ne a ranar Laraba.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Abbas Tajudeen ya faɗi hakan ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 11 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dennis Idahosa ya zama mataimakin gwamna
Dennis Idahosa, wanda ya wakilci mazabar Ovia a majalisar, an zaɓe shi mataimakin gwamnan jihar Edo a zaɓen gwamnan da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
An rantsar da shi tare da Gwamna Monday Okpebholo a ranar, 12 ga watan Nuwamban 2024.
Kujerarsa ta majalisa ta zama babu kowa a kanta
A cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar ya karanta a zauren majalisar, Julius Ihonvbere ya buƙaci majalisar da ta bayyana kujerar a matsayin wacce babu kowa a kanta.
Ya bayyana cewa hakan zai ba da dama domin fara aikin zaɓen wanda zai maye gurbinsa da zai wakilci mutanen Ovia.
Duk da kujerar Idahosa, a yanzu majalisar na da kujeru kusan huɗu wadanda ake sa ran hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta gudanar da sabon zabe.
Gwamna ya kasa fadin kasafin kuɗi
A wani labarin kuma, kun ji cewa abubuwa sun daburcewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, yayin gabatar da kasafin kuɗi a zauren majalisar dokoki.
Gwamnan dai ya gagara faɗin jimillar kasafin kuɗin na shekarar 2025 inda ya nuna cewa adadin ya sanya shi ya shiga ruɗu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng