Nasarawa: Ma'aikata Za Su Fara Walwala da Gwamna Ya Yi alkawarin Biyan N70,500

Nasarawa: Ma'aikata Za Su Fara Walwala da Gwamna Ya Yi alkawarin Biyan N70,500

  • Gwamna Abdullahi Sule ya tabbatar da cewa za a fara biyan sabon albashin N70,500 ga ma'aikatan Nasarawa a watan Disamba
  • Sule ya roki ma'aikatan gwamnatin Nasarawa su yi hakuri su janye yajin aikin da suka fara, wanda ya tsayar da komai a jihar
  • Gwamna Sule ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen inganta rayuwa da walwalar al'umma ciki har da ma'aikata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ba da tabbacin za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin da aka amince da shi watau N70,500 a watan Disamba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata ke ci gaba da yajin aiki a jihar wanda ya kai ga rufe dukkanin ofisoshin gwamnati a fadin Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Ma'aikatan Nasarawa za su fara. karɓan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,500 a watan Disamba Hoto: @whitenigerian
Asali: Twitter

Leadership ta ce Sule ya yi wannan alkawarin ne a wurin kaddamar da ofishin mataimakin gwamna, Dakta Emmanuel Akabe da aka sabunta a garin Lafiya.

Kara karanta wannan

NLC ta matsawa gwamna, ya amince N80,000 ya zama sabon mafi ƙarancin albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule zai sa ma'aikatan gwamnati walwala

Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta rayuwa da walawalar al’ummar jihar Nasarawa ciki har da ma’aikata, rahoton The Nation.

Ya ce matakin fara biyan albashin ya kara tabbatar da kudirin gwamnatinsa na inganta walwalar ma'aikata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Gwamnan Nasarawa ya rarrashi ma'aikata

Ya bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su sake tunani, kana su koma bakin aiki domin a wannan watan za a fara biyan mafi karancin albashi na Naira 70, 500.

Abdullahi Sule ya kuma yi wa ma'aikatan alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da biyan albashi yadda ta saba a duk karshen wata ba tare da samun jinkiri ba.

Yadda ma'aikata suka fara yajin aiki

Ma’aikatan sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani ne sakamakon gazawar gwamnatin Nasarawa na aiwatar da dokar mafi karancin albashi na N70,000.

Karkashin jagorancin ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC, ma'aikatan sun rufe ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin tilasta biyan buƙatunsu.

Kara karanta wannan

Albashin N70,000: Rikici ya balle tsakanin PDP da 'yan kwadago a jihar Kebbi game da albashi

Gwamnatin Bayelsa ta amince da N80,000

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bayelsa ta amince za ta fara biyan ma'aikatan kananan hukumomi N80,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Muƙaddashin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo ya sanar da haka a taron kwamitin aiwatar da dokar albashi a gidan gwamnati da ke Yenagoa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262