NLC Ta Matsawa Gwamna, Ya Amince N80,000 Ya Zama Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

NLC Ta Matsawa Gwamna, Ya Amince N80,000 Ya Zama Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

  • Gwamnatin Bayelsa ta amince za ta fara biyan ma'aikatan kananan hukumomi N80,000 a matsayin mafi karancin albashi
  • Muƙaddashin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo ya sanar da haka a taron kwamitin aiwatar da dokar albashi a gidan gwamnati da ke Yenagoa
  • Ya ce Bayelsa ba ta da ƙarfin tattalin arzikin da za ta bi tsarin gwamnatin tarayya wajen aiwatar da dokar albashin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Gwamnatin jihar Bayelsa karƙashin Gwamna Douye Diri ta amince da N80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon matsin lambar da take fuskanta daga ƙungiyoyin ƴan kwadago watau NLC da TUC.

Gwamna Diri na Bayelsa.
Gwamnatin Bayelsa ta amince za ta fara biyan ma'aikatan kananan hukumomi albashin N80,000
Asali: Twitter

Muƙaddashin gwamnan Bayelsa kuma mataimakin gwamna, Lawrence Ewhrudjakpo ne ya bayyana hakan ranar Talata, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Ma'aikata za su fara walwala da gwamna ya yi alkawarin biyan N70,500

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗi sabon albashin ne a wurin taron kwamitin sabon mafi karancin albashi da shugabannin kananan hukumomi takwas wanda aka yi a gidan gwamnati da ke Yenagoa.

Gwamna Diri ya gyara tsarin biyan N80,000

Muƙaddashin gwamnan ya ce gwamnati za ta aiwatar da sauye-sauyen da aka samu a tsarin mafi ƙarancin albashin a watan Disambar da muke ciki.

Ewhrudjakpo ya ce za a fara biyan ma'aikatan kananan hukumomo albashi mafi karanci N80,000 bayan amincewar masu ruwa da tsaki ciki har da ciyamomi.

"Mun amince cewa N80,000 ya zama sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kananan hukumomi," in ji shi.

Gwamnatin Bayelsa ta kara kuɗin fansho

Dangane da batun karin kudin fansho da gwamnatin tarayya ta ba da umarni, ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar Bayelsa za ta zauna ta yi nazari, Daily Trust ta rahoto.

Lawrence Ewhrudjakpo ya ce gabanin a cimma matsaya kan karin kudin fanshon, gwamnatin Douye Diri ta yi karin N10,000 a albashin ma'aikatan da suka yi ritaya.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta iya bin tsarin gwamnatin tarayya na aiwatar da sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata ba saboda ba ta da ƙarfin arziki.

NLC ta hakura da yajin aiki a Akwa Ibom

A wani rahoton, an ji cewa ƙungiyar kwadago rashen jihar Akwa Ibom ta fasa yajin aiki bayan Gwamna Umo Eno ya amince da N80,000 a mafi karancin albashi.

Shugaban NLC, Sunny James ya ce gwamnan ya kuma kara N32,000 a kuɗin da ake ba ma'aikatan da suka yi ritaya duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262