Gwamna Zai Tura Mata 1,000 Karatu a Fannin Lafiya, Zai Raba Kwamfutoci Miliyan 1
- Gwamnatin Neja ta fara shirin samar da kwamfutoci masu tarin yawa ga ɗaliban makarantun gwamnati a jihar
- Gwamna Umaru Bago ya fara shirin daukar nauyin karatun mata 1,000 kowace shekara domin karatu a fannin lafiya
- Umaru Bago ya fadi haka ne yayin wani taro da ya samu halartar manyan shugabanni da suka hada da mai alfarma sarkin Musulmi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta sanar da shirin rarraba kwamfutoci miliyan daya ga makarantun gwamnati a jihar.
Gwamnan jihar, Umaru Bago ne ya bayyana hakan yayin wani taron shugabannin gargajiya da na addini a Minna kan mahimmancin ilimin mata a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Hadimin gwamna Bago ya wallafa a Facebook cewa taron ya samu haɗin guiwa daga ma’aikatar ilimi ta kasa, shirin Agile, ma’aikatar ilimi ta jihar Neja da kuma gidauniyar Sultan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Samar da intanet a makarantun Neja
Gwamnan Neja ya bayyana cewa an riga an fara aikin sayen kayan aikin zamani domin bai wa ɗalibai damar amfani da fasahar zamani.
Ya ce an saka igiyoyin sadarwa na zamani domin samar da intanet kyauta ga makarantun gwamnati da sauran wurare, inda za a fara gwajin shirin a Minna nan ba da jimawa ba.
Za a ba mata 1,000 tallafin karatu a Neja
Gwamna Bago ya jaddada cewa gwamnati tana da tsare-tsaren bayar da tallafin karatu na shekara-shekara ga mata 1,000.
Gwamnatin Neja za ta rika daukar nauyin matan ne domin su yi karatun jinya, likitanci da sauran fannonin lafiya.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga sarakuna
Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini su jagoranci yaƙin neman ilimin mata a cikin al’ummominsu.
Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, wanda ya samu wakilcin Suraju Darda’u, ya bayyana muhimmancin shugabannin gargajiya da addini wajen wayar da kai game da ilimin mata.
Gwamna ya tallafawa mata a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta raba Naira miliyan 250 ga kungiyoyin mata domin bunkasa kanana sana'o'i.
Yain raba tallafin a Kontagora, gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa matan za su samu damar zama masu dogaro da kai da bunkasa tattali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng