Lokaci Ya Yi: Shugaban Karamar Hukuma Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsari
- Jihar Neja ta yi babban rashi, Allah ya yi wa shugaban ƙasar hukumar Katcha, Danlami Abdullah Saku rasuwa
- Danlami ya rasu ne sakamakon hatsarin motar da ya rutsa da shi a titin Minna-Suleja da misalin karfe 7:00 na daren ranar Talata, 10 ga watan Disamba
- Gwamna Muhammadu Umaru Bago ya yi alhinin rasuwar Ɗanlami, ya kuma yi ta'aziyya ga iyalansa, al'ummar Katcha da jihar Neja baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Shugaban karamar hukumar Katcha a jihar Neja, Danlami Abdullahi Saku ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya rutsa da shugaban karamar hukumar ne a kan titin Minna zuwa Suleja da misalin ƙarfe 7:00 na daren jiya Talata.
Shugaban ƙaramar hukumar Neja ya rasu
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Danlami Saku ya gamu da ajalinsa ne a yankin Kwakwuti da ke titin yayin da yake hanyar zuwa birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren watsa labaran Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja, Bologi Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Bologi ya ce Gwamna Bago ya kaɗu da jin labarin rasuwar ciyaman na Katcha, inda ya bayyana wannan rashin a matsayin mai taɓa zuciya da ban tausayi.
Ya ƙara da cewa rasuwar Danlami Saku, tunatarwa ce ga al'umma cewa dukkan talikai daga Allah su ke, kuma zuwa gare shi za su koma a lokacin da aka ɗibar masu.
Gwamna Bago ya miƙa sakon ta'aziyya
Bayan haka kuma Mai girma Gwamnan Umaru Bago ya miƙa sako jaje da ta'aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar karamar hukumar Katcha da Neja baki ɗaya bisa wannan rashi.
Ya kuma ja hankalin mutane da su kasance masu yi Allah madaukakin sarkin ɗa'a a kowane lokaci domin Shi mai cikakken iko ne a kan komai, rahoton Daily Trust.
Tsohon shugaban NLC ya mutu a Edo
A wani rahoton, an ji cewa tsohon shugaban NLC a jihar Edo, Kwamared Kaduna Eboigbodin ya mutu bayan wata ƴar hatsaniya da ƴan sanda a Benin.
An ruwaito cewa wasu ƴan sanda ne suka tare shi, suka hana shi wucewa lamarin da ya harzuka shi ya faɗi ƙasa matacce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng