NLC Ta Yi Fatali da Zancen Fara Biyan Mafi Karancin Albashin Ma'aikata a 2025

NLC Ta Yi Fatali da Zancen Fara Biyan Mafi Karancin Albashin Ma'aikata a 2025

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bayyana rashin gamsuwa da matakin da mahukuntan FCT ke son dauka a kan albashi
  • Hukumomin sun yi wa ma'aikatan kananan hukumomin tayin fara biyansu mafi karancin albashi a karshen watan Janairu
  • Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) reshen FCT, Abdullahi Kabir ya ce hakan ya saba ka'ida

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta a Babban Birnin Tarayya ya shiga rana ta 11 a kan batun fara biyan mafi karancin albashi.

Tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da shugabannin kananan hukumomi na ci gaba da samun cikas kan lokacin fara biyan mafi karancin albashi na N70,000.

Jarida
NLC za ta ci gaba da yajin aiki a FCT Hoto: NLC Headquarters
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) reshen FCT, Abdullahi Kabir, ya bayyana rashin jin dadin tayin mahukunta.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fahimci halin da ake ciki, ta taso bankin CBN a gaba kan takardun kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar NLC ta fusata kan biyan albashi

Kungiyoyin kwadago sun bayyana rashin gamsuwa da fara biyan ma'aikatan kananan hukumomi a Abuja mafi karancin albashi a Janairu, 2025.

Kungiyar kwadago ta ce a watan Disamba, 2024 ya kamata a fara biyan ma'aikatan kudinsu maimakon farkon 2025 da mahukuta ke cewa za su fara biyan kudin.

'Yan NLC su na kuka da gwamnati

Kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa jinkirin fara biyan har zuwa Janairu zai ƙara bashin alawus zuwa wata biyar, yayin da fara biyan a Disamba zai rage bashin zuwa wata hudu.

Kungiyar ta jaddada wasu ƙorafe-ƙorafe, ciki har da rashin samun alawus na musamman ga ma’aikatan kananan hukumomi da sauran hakkokinsu.

Kungiyar NLC ta janye yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta bayyana janye yajin aikin da ta tsunduma biyo bayan amincewar gwamnatin Akwa Ibom na cika masu burinsu.

Kara karanta wannan

Albashin N70,000: Rikici ya balle tsakanin PDP da 'yan kwadago a jihar Kebbi game da albashi

Gwamnatin Umo Eno ta tabbatar da za ta fara biyan ma'aikatan jihar mafi karancin albashin N80,000 bayan gwamnatin tarayya ta amince da biyan N70,000 ga ma'aikatan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.