Za a Zamanantar da Hudubar Juma'a a Masallacin Abuja, An Kara Limamai 5

Za a Zamanantar da Hudubar Juma'a a Masallacin Abuja, An Kara Limamai 5

  • Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta sanar da karin limamai biyar a Masallacin Abuja
  • Karin limaman sun hada da mazauna garin Abuja da kuma masu ziyara daga jihohi daban-daban lokaci bayan lokaci
  • NSCIA ta bayyana shirin amfani da fasaha domin fassara hudubar Juma’a kai tsaye cikin harsuna daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta sanar da karin limamai biyar ga Masallacin Abuja a wani taro da aka gudanar a ranar Talata.

A cewar majalisar, matakin na daya daga cikin kokarin karfafa sashen kula da harkokin addini a masallacin, tare da fadada ayyukan ibada da yada ilimi.

Abuja
An nada sababbin limamai a masallacin Abuja. Hoto: National Supreme Council for Islamic Affairs
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa sakataren NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa karin limaman na da nufin tabbatar da daidaito da kuma bai wa kowa damar shiga ayyukan addini cikin sauki.

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin limamai 5 a Masallacin Abuja

Jaridar the Cable ta wallafa cewa NSCIA ta sanar da limamai biyar, guda biyu 'yan kabilar Ibo kuma kwamitocin GPC da NFC masu lura da masallacin sun tabbatar da su:

  • Farfesa Ilyasu Usman daga jihar Enugu (mai ziyara)
  • Farfesa Luqman Zakariyah daga jihar Osun (mazaunin Abuja)
  • Dr Abdulkadir Salman daga jihar Kwara (mai ziyara)
  • Barista Haroun Muhammad Eze daga jihar Enugu (mazaunin Abuja)
  • Farfesa Khalid Aliyu Abubakar daga jihar Filato (mai ziyara)

An bayyana cewa wadanda ke zaune a Abuja za su kasance cikin ayyuka na yau da kullum, yayin da masu ziyara za su zo daga jihohin su lokacin da ake bukatar su.

Aiki da fasahar zamani domin fassara huduba

Sakatare Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa ana shirin inganta hudubobin Juma’a ta hanyar fasahar zamani.

Hudubar masallacin za ta kasance cikin harshen Larabci, amma masu ibada za su iya amfani da na'ura domin jin fassarar cikin Hausa, Turanci, Igbo ko Yarbanci.

Kara karanta wannan

Shugaban masu garkuwa da mutane, Idris Alhaji Jaoji ya shiga hannu

Farfesa Oloyede ya bayyana cewa matakin zai rage bukatar sanya lokuta daban domin fassara bayan hudubar.

Za a kara limamai a masallacin Abuja

NSCIA ta yi bayanin cewa za a iya kara limamai nan gaba, musamman daga yankin Kudu maso Kudu da har yanzu ba su samu wakilci.

An kuma tabbatar da cewa limaman za su taimaka wajen gudanar da abubuwa daban-daban da za su inganta addini da tsare-tsaren masallacin.

Peter Obi ya taya limamin Abuja murna

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya taya sabon limanin masallacin Abuja murna.

Peter obi ya bayyana nadin Farfesa Iliyasu Usman a matsayin limamin masallacin kasa babban cigaba kasancewar shi ne dan kabilar Ibo na farko da ya rike matsayin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng