Yahaya Bello: Dino Melaye Ya Yi Wa Tsohon Gwamnan Kogi Shagube kan zuwa Gidan Kaso
- Sanata Dino Melaye ya taso tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gaba bayan kotu ta tura shi gidan gyaran hali na Kuje
- Tsohon sanatan ya bayyana cewa dama a baya ya taɓa yin hasashen cewa Yahaya zai ƙare a gidan kaso idan ya kammala mulki
- Kalaman Dino Melaye dai na zuwa ne bayan babbar kotu tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare Yahaya Bello a kurkuru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Tsohon ɗan majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye, ya yi magana kan tsare Yahaya Bello da aka yi a gidan gyaran hali na Kuje.
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa ya yi hasashen hakan za ta kasance da tsohon gwamnan na Kogi, shekara shida da suka wuce.
Dino Melaye ya taso Yahaya Bello a gaba
Dino Melaye, wanda jigo ne a jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kogi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a daren ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sanatan ya sanya wani bidiyonsa inda yake waƙa da harshen Yarbanci cewa Yahaya Bello zai tsinci kansa a gidan yari bayan ya gama mulkin jihar Kogi na shekara takwas.
A tare da faifan bidiyon, tsohon sanatan ya rubuta cewa:
"Shekara shida da suka gabata, Sanata Dino Melaye ya yi hasashen cewa Yahaya Bello zai ƙare a gidan yari. A yau, zai yi bikin Kirsimeti a kurkukun Kuje. Mulki na Allah ne."
Dino Melaye da Yahaya Bello dai sun kasance abokan hamayyar siyasa tun a shekarar 2016, jim kaɗan bayan Yahaya Bello ya zama gwamnan jihar Kogi.
Melaye ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda ba sa ga maciji da tsohon gwamnan a lokacin da yake kan mulki.
EFCC ta cafke Yahaya Bello
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.
Jami'an na hukumar EFCC sun tsare Yahaya Bello a hedkwatar hukumar ta ƙasa da ke babban birnin tarayya, bayan sun cafke shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng