'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Samu Nasarori a Kaduna
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, sun samu nasarori kan masu tayar da ƙayar baya
- Ƴan sandan sun daƙile yunƙurin kai hari na ƴan bindiga tare da cafke wasu da ake zargi da yin fashi da makami
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, wanda ya bayyana hakan ya ce an samu nasarorin ne bayan samun bayanan sirri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sanar da samun nasarori kan ƴan bindiga da ƴan fashi da makami.
Jami'an ƴan sandan sun hallaka ɗan bindiga ɗaya, sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da cafke wasu ƴan fashi guda uku.

Asali: Original
Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun samu nasara kan ƴan bindiga

Kara karanta wannan
Ana fama da karancin kudi, 'yan sanda sun cafke masu samar da kudaden bogi a Kano
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa an kuma ƙwato makamai a yayin samamen da aka kai kan miyagun a lokuta daban-daban.
Ya bayyana cewa an kai samamen ne a tsakanin ranakun, 8 zuwa 10 ga watan Disamban 2024 bayan an samu bayanan sirri.
"A ranar 9 ga watan Disamba, jami'an ƴan sanda da ke Dan Magaji sun cafke mutum uku a kan titin Kaduna-Kano. An gano harsasai masu kaurin 9mm guda 216 da harsashi ɗaya mai kaurin 7.62mm a hannunsu."
"Haka kuma a ranar 10 ga Disamba, DPO na ƴan sanda a Damakasuwa ya kai ɗauki bayan samun bayanai kan harin ƴan bindiga a ƙauyen Tudu Gishere.
"An ɗaƙile harin sakamakon haɗin gwiwa tsakanin ƴan sanda, ƴan banga da jami'an CJTF. An kashe ɗan bindiga ɗaya yayin da sauran suka tsere ɗauke da raunuka."
- ASP Mansir Hassan
Jami'an yan sanda sun ceto mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Taraba, sun samu nasarar ceto wasu mutane guda uku da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
Jami'an ƴan sandan sun ceto mutanen ne a Dutse Mubayu, kusa da tsaunin Kona na Jalingo, babban birnin jihar Taraba bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng