Majalisa Ta Fahimci Halin da Ake Ciki, Ta Taso Bankin CBN a Gaba kan Takardun Kuɗi
- Majalisar Wakilai ta sa baki kan ƙarancin takardun kudin da ake fama da shi a ƴan kwanakin nan a Najeriya
- A zaman ranar Talata, 10 ga watan Disamba, majalisar ta bukaci bankin CBN ya magance matsalar cikin gaggawa
- Majalisar ta kuma ba kwamitin harkokin banki mako guda ya gudanar da bincike kan lamarin sannan ya haɗa rahoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta nuna damuwa kan karancin takardun kudin da ake fama da shi a bankunan kasuwanci da ke faɗin kasar nan.
Hakan ya sa Majalisar ta yi kira ga babban bankin kasa watau CBN ya gaggauta magance wannan matsala da ta kara jefa ƴan Najeriya cikin wahala.
Hon. Uguru Emmanuel shi ne ya gabatar da kudirin gaggawa kan karancin Naira a zaman yau Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yadda ake fama da karancin Naira' - Majalisa
Ɗan Majalisar ya ja hankalin abokan aikinsa kan tasirin da ƙarancin kudin ke haifarwa a tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
Ya ce lamarin ya sa ƴan Najeriya ba su iya samun tsabar kudi ko da kuwa wanda za su biya bukatun yau da kullum.
Hon. Emmanuel ya bayyana cewa a watan Disamba, 2022, CBN ya kayyade adaɗin cire kudi, N500,000 ga ɗaiɗaikun jama'a da N5m ga kamfanoni.
Ya ce a yanzu bankuna sun yi fatali da wannan tsarin, sun dawo N10,000 kaɗai suke ba mutane ko kuma su hana mutum ko sisi.
Ƙarancin Naira: Kasuwa ta buɗewa masu POS
Ɗan majalisar ya kuma nuna damuwa kan alakar bankuna da masu POS, wanda ya ce suna da hanyar samun tsabar kuɗi yadda ransu ke so kuma su karbi kuɗi da tsada.
"A ina masu POS suke samuj tsabar kudi yayin da aka nema aka rasa a bankuna?" in ji shi.
Dan majalisar ya yi gargadin cewa matukar dai CBN bai dauki matakin gaggawa ba, lamarin na iya kara muni, musamman yadda ƙarshen shekara ya gabato.
Majalisar Wakilai ta ɗauki mataki
Bisa haka, majalisar ta umurci kwamitin da ke kula da harkokin banki da ya binciki batun karancin kudi a bankuna kana ya kawo rahoto a cikin mako ɗaya.
Ta kuma umarci CBN ya gagaguta magance matsalar ƙarancin kudi a hannun jama'a, rahoton Punch.
Majalisa ta yi barazana ga wasu hukumomi
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa za ta hana wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya kasafin kudin shekarar 2025.
An yi barazanar ga dukkanin hukumomin da suka ki bayyana domin kare kasafin kudin da gwamnati ta ware masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng