Ana Fama da Karancin Kudi, 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kudaden Bogi a Kano

Ana Fama da Karancin Kudi, 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kudaden Bogi a Kano

  • Dubun wasu mutane masu ɗauke da kuɗin bogi ta cika a jihar Kano bayan jami'an rundunar ƴan sanda sun cafke su
  • Jami'an ƴan sandan sun cafke mutanen ne su uku bayan an samu kuɗaɗen bogi da suka kai jimillar N129bn a hannunsu
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya ce mutanen na ci gaba da ba da bayanai a binciken da ake yi domin gano masu samar da kuɗaɗen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kuɗaɗen bogi.

Jami'an ƴan sandan sun cafke mutanen ne bisa zargin mallakar kuɗaɗen bogi da suka kai N129,542,826,000:00.

'Yan sanda sun cafke masu kudaden bogi a Kano
'Yan sanda sun kama masu kudaden bogi a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Talata, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun samu nasarori a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun kama masu kuɗaɗen bogi a Kano

Haruna Kiyawa ya bayyana cewa kuɗin sun haɗa da Dalar Amurka da CFA da Naira, da kuma waɗanda aka sato daga hannun wani dillali, rahoton The Punch ya tabbatar.

"An ƙwato kuɗin jabu kwatankwacin jimillar N129,542,823,000:00 daga hannun waɗanda ake zargi."

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa kuɗin jabun sun haɗa da $3,366,000, CFA51,970,000 da kuma N1,443,000.

Ya ƙara da cewa an kama mutane biyun da aka samu da kuɗin da kuma wanda suka sato a hannunsa.

Abdullahi Kiyawa ya ce a halin yanzu suna hannun ƴan sanda inda suke taimakawa wajen gudanar da bincike, domin gano ainihin waɗanda suke buga kuɗaɗen bogin.

Ƴan sanda sun ƙi karɓar cin hanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'an rundunar ƴan sandan jihar Rivers sun tsallake cin hancin $17,000 da aka ba su, bayan sun cafke wasu masu laifi.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya yabi Tinubu ana batun kudirin haraji

Waɗanda aka cafken dai masu laifin damfarar yanar gizo ne waɗanda suka daɗe suna aikata wannan baƙar sana'ar ta yaudarar mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng