Ana Rigimar Haraji, Tinubu Ya Nada Mukaddashin Akanta Janar na Gwamnatin Tarayya

Ana Rigimar Haraji, Tinubu Ya Nada Mukaddashin Akanta Janar na Gwamnatin Tarayya

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada sabon mukaddashin babban mai kula kudin Gwamnatin Tarayya
  • Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi ne saboda kwarewar da yake da shi kan lissafe-lissafen kudi a Najeriya
  • Wannan na kunshe a wata sanarwa da hadimin shugaban kasar a bangaren sadarwa da tsare-tsare ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da nadin sabon mukaddashin Akanta-janar na Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi a matsayin Akanta-janar na Gwamnatin Tarayya a yau Talata 10 ga watan Disambar 2024.

Tinubu ya nada sabon mukaddashin Akanta-janar a Najeriya
Bola Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi a matsayin mukaddashin Akanta-janar a Najeriya. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Tinubu ya nada sabon Akanta-janar a Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya sanar da nadin Ogunjimi a matsayin mukaddashin Akanta-janar na Tarayya biyo bayan ritaya da tsohon mai rike da mukamin ya yi.

Tsohon Akanta-janar din mai suna Oluwatoyin Madein ya tafi hutu ne kafin ya yi ritaya a ranar 7 ga Maris din 2024.

A cewar sanarwar da Onanuga ya fitar nadin Ogunjimi ya fara aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.

“Da yake sanar da wanda zai gaji Madein, Tinubu ya tabbatar da sauyi a shugabancin baitulmali tare da tabbatar da cigaba da aiwatar da manufofin gyaran baitulmali na wannan gwamnati."
“Shamseldeen Ogunjimi, wanda ke matsayin babban jami’in ma’aikata a ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), yana da kwarewar sama da shekaru 30 a fannin gudanar da harkokin kudi."
“Ogunjimi ya samu horo a matsayin akanta kuma masani kan binciken damfara da dillancin hannun jari da kwararre a harkokin tsaro da zuba jari."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga uku, sabon hafsan rundunar sojojin Najeriya ya kama aiki

- Cewar sanarwar

Ogunjimi ya kammala karatun digirin farko da na biyu a fannin lissafin kudi da kuma wanda ya shafe shekaru yana aiki.

Shugaba Tinubu ya ba yan adawa shawara

Kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna muhimmancin da zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya.

Tinubu ya buƙaci ƴan adawa da su rungumi zaman lafiya domin ƴan Najeriya abu ɗaya ne duk da bambancin da suke da shi a siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.