An Tono Sirrin Alakar Tinubu da Akpabio a Wani Taron Sanatoci a Abuja

An Tono Sirrin Alakar Tinubu da Akpabio a Wani Taron Sanatoci a Abuja

  • Shugaban masu rinjaye a majalisa ya ce Bola Tinubu yana samun natsuwa saboda Godswill Akpabio ne shugaban majalisar dattawa
  • Sanata Bamidele ya jinjinawa Godswill Akpabio kan salon jagorancinsa wanda ke hade kan 'yan majalisar a ko da yaushe
  • Haka zalika, Sanata Adams Oshiomhole ya ce Akpabio yana nuna kwarewa wajen hada kai da jure muhawara a zauren majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa Bola Tinubu na samun kwanciyar hankali a mulkinsa saboda jagorancin Godswill Akpabio

Sanata Opeyemi Bamidele ya fadi haka ne yayin bikin cika shekara 62 da haihuwar Godswill Akpabio, wanda ya gudana a Abuja ranar Litinin.

tinubu
Sanata ya fadi alakar Tinubu da Akpabio. Hoto: Bayo Onanuga|Nigerian Senate
Asali: Facebook

Rahoton The Cable ya nuna cewa Bamidele ya ce Akpabio ya samu gagarumar nasara wajen jagorancin majalisar ta yadda ya hada kawunan sanatoci domin cimma muradun dimokradiyya.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji da abubuwa 9 da suka yi wa gwamnatin Tinubu illa a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bamidele: 'Tinubu ya aminta da Akpabio'

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa Tinubu yana samun bacci cikin kwanciyar hankali ne saboda yarda da ya yi da shugabancin Akpabio.

Tribune ta wallafa cewa Bamidele ya ce sanatoci suna alfahari da jagorancin Akpabio, wanda ke zama misali ga shugabanci mai inganci.

Oshiomhole ya yabi jagorancin Akpabio a majalisa

Sanata Adams Oshiomhole, wanda ke wakiltar Edo ta Arewa, ya jinjinawa Akpabio kan yadda yake hada kan sanatoci da jure muhawara.

"Shugabancin majalisar dattawa yana bukatar jagora mai karfin zuciya, wanda zai iya jure muhawara da tabbatar da cigaban dimokradiyya."

- Adams Oshiomhole

Sanata Oshiomhole ya kuma bayyana cewa Akpabio ya nuna kwarewa wajen tabbatar da zaman lafiya a majalisar, duk da bambance-bambancen ra'ayi a lokutan muhawara.

An yi taron ne domin mika sakon taya murna ga Akpabio, tare da yaba masa bisa yadda ya jagoranci majalisar dattawa zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Daga dawowa Najeriya, Tinubu ya shiga yin nade naden mukami a hukumar raya Arewa

Matasan Najeriya sun dura kan Akpabio

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya sun dura kan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio kan maganganun da ya yi musu.

Sanata Godswill Akpabio ya shiga tarkon matasan Najeriya ne bayan magana da ya yi a kan tsadar rayuwa da suke gani kamar cin fuska ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng