A Karo na 6, Kotu Ta Sake Ingiza Keyar Mama 'Boko Haram' zuwa Kurkuku

A Karo na 6, Kotu Ta Sake Ingiza Keyar Mama 'Boko Haram' zuwa Kurkuku

  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCF) ta maka Aisha Wakil a gaban kotun da ke Borno
  • Lamarin ya biyo bayan zarginta da wasu mutum biyu daga cikin kungiyarta da damfarar wani motar miliyoyin Naira
  • Kotu ta yanke mata hukuncin shekaru a gidan yari, wanda ya zama karo na shida a ake yanke mata hukuncin dauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Babbar kotun jihar Borno da ke Maiduguri ta sake yankewa Aisha Wakil, wadda aka fi sani da Mama Boko Haram, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.

Wannan shi ne kari na shida da aka yankewa fitacciyar matar hukuncin dauri bisa zarge-zarge mabambanta, daga ciki har da damfara.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

Haram
Kotu ta daure Mama Boko Haram Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a wannan karon, an daure Aisha Wakil ne bisa zargin zambar wasu makudan kudade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta daure Mama Boko Haram

Dazu jaridar Daily Post ta wallafa cewa kotu ta daure Aisha Wakil da wasu mutum biyu daga cikin ‘yan kungiyarta ta Complete Care and Aid Foundation.

Jami’an biyu sun hada da manajan shirye-shiryen kungiyar, Tahiru Daura, da kuma daraktan kungiyar na kasa, Prince Shoyode, inda aka yanke masu hukuncin daurin shekaru biyar-biyar.

Dalilin daure Mama Boko Haram da jama’arta

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar Aisha Wakil da sauran mutanen gabab kotu bisa zargin yaudarar Bukar Kachalla.

EFCC ta zarge su da damfarar Bukar Kachalla na Abks Ventures, ta hanyar yaudarar sa don ya ba su motar Toyota Camry samfurin 2012 ta N6m, amma aka hana shi kudinsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

Sojoji sun fatattaki 'yan Boko Haram

A baya kun ji cewa zaratan sojojin kasar nan sun yi luguden wuta a kan wasu miyagun 'yan kungiyar Boko Haram a lokacin da su ke tsaka da gudanar da taronsu a Borno.

Rundunar ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri da ke bankado masu wurin da 'yan kungiyar ke shirin gudanar da taronsu, inda aka yi nasarar hallaka da dama daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.