Kotu Ta Yanke Hukunci: Tsohon Gwamnan Kogi Zai Shafe Kwana 46 a Gidan Yarin Kuje
- Kotun tarayya ta iza keyar Yahaya Bello zuwa gidan yarin Kuje bayan ta ki amincewa da bukatar belin da tsohon gwamnan
- Tsohon gwamnan na Kogi yana fuskantar tuhume tuhume 16 da EFCC ta shigar kan zargin karkatar da kimanin N110bn a ofis
- Alkaliyar kotun ta dage sauraron karar zuwa 25 ga Fabrairun 2025, wanda ke nufin Yahaya Bello zai shafe kwanaki 46 a tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello zai fara kirga kwanakinsa a gidan kurkukun Kuje bayan gurfanarsa gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello da wasu a gaban kotun tarayyar a ranar Talata kan tuhumar karkatar da kimanin N110bn.
Kotu ta garkame Yahaya Bello a kurkuku
Rahoton Channels TV ya nuna cewa babbar kotun tarayya da ke Maitama ta umarci a tsare tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a gidan yarin Kuje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’a Maryann Anenih ta bayar da wannan umarni bayan dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Fabrairu, 2025.
Wannan ci gaban ya biyo bayan kin amincewar kotu da bukatar belin da Yahaya Bello ya shigar kafin a yanke hukunci a kan shari'arsa.
Yahaya Bello na fuskantar tuhume-tuhume 16
Yahaya Bello, wanda ya jagoranci mulkin jihar Kogi daga 2016 zuwa 2024, yana fuskantar shari’a kan zargin karkatar da N110bn.
EFCC ta gurfanar da shi a kan tuhume tuhume 16 tare da wasu jami’an gwamnatin Kogi biyu: Umar S. Oricha da Abdulsalami Hudu.
Tsohon gwamnan yana hannun EFCC tun a ranar 25 ga Nuwamba, bayan mika kansa da ya yi ga hukumar a karo na biyu.
Kotu ta hana belin Yahaya Bello
Tun da fari, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta ki amincewa da bukatar lauyoyin Yahaya Bello na ba da belin tsohon gwamnan.
Mai Shari'a Maryann Anenih ta babbar kotun ta yanke hukuncin cewa an shigar da bukatar ba da belin Yahaya Bello da wuri, don haka babu cancantar ba da belin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng