'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarin Wuta a cikin Gari, Sun Yi Garkuwa da Hadimin Tsohon Gwamna

'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarin Wuta a cikin Gari, Sun Yi Garkuwa da Hadimin Tsohon Gwamna

  • 'Yan bindiga sun kutsa har cikin ofis, sun yi awon gaba da hadimin tsohon gwamnan jihar Kogi da yammacin ranar Litinin
  • Rahoto daga yankin ya nuna cewa maharan sun farmaki wani wurin sayar da abinci na mutumin, suka shiga har ofishinsa
  • Har yanzun ƴan bindigar ba su tuntuɓi iyalansa don neman kudin fansa ba, lamarin da ya sa ake fargabar halin da yake ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Kabiru Onyene, hadimin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Rahotannin da suka fito daga yankin yau Talata sun nuna cewa maharan sun sace Kabiru Onyene da misalin karfe 7:05 na yammacin ranar Litinin.

Hon. Kabiru Onyene
Yan bindiga sun yi awon gaba da hadimin tsohon gwamnan jihar Kogi Hoto: Hon. Kabiru Onyene
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka sace Kabiru Onyene

Ƴan bindigar sun farmaki ofishinsa da ke Okene, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kana suka tasa shi zuwa cikin jeji, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabiru na cikin hutawa da wani wurin sayar da abincinsa 'Nahaziyat' da ke kusa da fadar marigayi Ohinoyi na Ebiraland lokacin da maharan suka kutsa kai.

Wani ganau ya bayyana cewa maharan sun harbi mutum ɗaya kuma yanzu haka yana kwance ana yi masa magani a asibiti rai hannun Allah, rahoton The Sun.

Ƴan bindiga sun yi ɓarin wuta a harin

Mutumin mai suna, Ozovehe ya ce:

"Muna zaune da misalin karfe 7:05 na yammacin Litinin, ba zato muka fara jin wani sauti, mafi yawan mutane sun ɗauka sautin masu ba da nishaɗi ne da ke nuna bikin Kirsimeti ya matso.
"Amma da muka ga mutane na gudun neman tsira muka gane ashe sautin harbin bindiga ne. Bayan haka labari ya fara yaɗuwa cewa ƴan bindiga sun shiga ofishin Kabiru sun tafi da shi.

Wasu majiyoyin sun ce har yanzun masu garkuwa ba su tuntuɓi iyalansa ba, wanda hakan ya haifar da fargaba kan dalilin sace shi da kuma yanayin lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi fatali da kudin fansa, sun fadi dalilin raina Naira miliyan 3

Wasu yan bindiga sun sace kansila a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace kansila da wasu mutane a yankin karamar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi.

Satar mutanen ta biyo bayan kama wasu mutum uku a mako guda da ya gabata a yankin, ciki har da wani yaro dan shekara takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262