Tsohon Mai ba Jonathan Shawara Ya Fadi Abin da Zai Faru da Tattalin Najeriya Kwanan Nan

Tsohon Mai ba Jonathan Shawara Ya Fadi Abin da Zai Faru da Tattalin Najeriya Kwanan Nan

  • Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yabi manufofin da Bola Tinubu ya shigo da su
  • Ya bayyana cewa akwai kwararan alamu da ke nuna cewa tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na haifar da da mai idanu
  • Tsohon hadimin ya lissafo wasu daga cikin sassan da aka fara ganin ci gaban manufofin gwamnatin APC a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Reno Omokri ya kwantar da hankalin ‘yan Najeriya a kan tsare-tsaren tattalin arziki.

Ya bayyana cewa gyaran tattalin arziki na shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ke yi zai samar da makoma mai kyau ga kasar nan sannu a hankali.

Tinubu
Reno Omokri ya ce tattalin arziki na ci gaba Hoto: Reno Omokri/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Reno Omokri ya fadi haka ne ta cikin sanarwar da ya fitar a kan ci gaban tattalin arzikin da kasar nan ke samu a yanzu.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tsarin Tinubu zai cicciba kasa,” Omokri

Jaridar Blueprint ta wallafa cewa kamata ya yi ‘yan Najeriya su rika murna da ci gaban da tattalin arzikin kasar su ke samu a yanzu.

Reno Omokri ya ce;

“Kamata ya yi mu yi murna da ci gaban GDP 3.46%, ƙididdigar rashin aikin yi ya ragu zuwa 4.3%, an samu ribar kasuwanci ta Naira tiriliyan 5.8 a zangon karshe na shekara, gyaran matatar mai ta Fatakwal, da kuma samun karuwar darajar Naira a kasuwannin duniya.”

Tinubu: Omokri ya shawarci ‘yan Najeriya

Reno Omokri ya bayyana cewa akwai hujjoji masu yawa da ke nuna cewa tattalin arziki yana kan tafarkin bunkasa da kawo cigaba.

Ya kara da cewa wasu daga cikin gyare-gyaren da aka yi kamar soke tallafin mai ya bai wa gwamnati damar samun karin kudi da za a yi amfani da su wajen magance bukatun al’umma.

Omokri ya yi murna da farfadowar Naira

Kara karanta wannan

Karfin Naira: Ƴan canji sun lissafa abubuwa 3 da suka jawo dalar Amurka ta karye

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana farin ciki bisa yadda farashin Naira ke ci gaba da hauhawa a kasuwar musayar kudade.

Ya bayyana takaicin yadda wasu daga cikin 'yan kasar nan ke bakin ciki da ci gaban da ake samu, musamman saboda sun yi cacar da nasararsu za ta samu ne idan Naira na faduwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.