Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Fatali da Bukatar Belin Tsohon Gwamnan Jihar Kogi
- Kotu ta hana belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello saboda an shigar da buƙatar tun kafin a kama shi ko gurfanar da shi
- Mai Shari'a Maryann Anenih ta ce doka ta amince a bada belin wanda ake tuhuma ne idan yana hannu ko kuma ya gurfana a gaban kotu
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello ne ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024 kwana ɗaya bayan kama shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yi watsi da bukatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.
Alƙalin kotun, Mai Shari'a Maryann Anenih ce ta yanke wannan hukuncin, inda ta bayyana cewa an shigar da bukatar belin da wuri.
Kotu ta hana belin tsohon gwamnan Kogi
Mai shari'ar Anenih ta yi fatali da bukatar belin tsohon gwamnan ne saboda an shigar da ita kafin ya gurfana a gabanta, kamar yadda Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya Bello na fuskantar shari'a a gaban kotun ne kan tuhume-tuhumen da suka shafi zargin karkatar da wasu kuɗaɗe kimanin Naira biliyan 110.
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da Yahaya Bello tare da wasu mutum biyu, rahoton Daily Trust.
Kotu ta yanke hukunci kan beli
Yayin da take yanke hukuncin, mai shari'a Maryann Anenih ta ce:
"Takardar neman belin ta nuna cewa an shigar da bukatar ne ranar 22 ga watan Nuwamba, kwanaki kafin cafke wanda ake tuhuma na farko watau Yahaya Bello.
Da take karanta sashen ACJa, alkalin ta ce doka ta tanadi cewa za a iya bayar da belin wanda ake tuhuma idan yana tsare ko kuma aka gurfanar da shi a gaban kotu.
Dalilin hana belin Yahaya Bello
Yahaya Bello ya shigar da bukatar neman beli ne a ranar 22 ga watan Nuwamba kuma an tsare shi a ranar 26 ga watan Nuwamba, washe gari aka gurfanar da shi ranar 27 ga watan Nuwamba.
Kotun ta kuma bayar da belin wanda ake kara na biyu, Umar Oricha a kan kudi Naira miliyan 300 tare da sharaɗin kawo waɗanda za su tsaya masa mutum biyu.
Kotu ta yi fatali da bukatar hukumar EFCC
Rahoto ya gabata cewa babbar kotun tarayya ta watsi da bukatar EFCC na ci gaba da zaman shari'ar tsohon gwamnan Kogi duk da babu lauyoyinsa.
Alkalin kotun ya bayyana cewa idan aka yi haka. ba a yi masa adalci ba, inda ya ba da lokacin don a tura sako ga lauyoyin Yahaya Bello.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng