‘Ka Saɓa da Annabi’: Malamin Musulunci Ya Dura kan Sanusi II bayan Kalamansa

‘Ka Saɓa da Annabi’: Malamin Musulunci Ya Dura kan Sanusi II bayan Kalamansa

  • Malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya shawarci wani sarki da ya ji tsoron Allah SWT kan kalamansa
  • Malamin ya ce abin takaici ne yadda basaraken da ke ikirarin ilimin addini zai furta cewa mata su rama idan mazajensu sun mare su
  • Hakan na zuwa ne bayan Sarki Muhammadu Sanusi II ya maimaita cewa duk matar da mijinta ya mare ta, to ta rama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya ya nuna damuwa kan kalaman wani sarki game da rayuwar aure.

An ji Sarki Muhammadu Sanusi II yana cewa duk matar da mijinta ya mare ta, lallai ta rama ba tare da bata lokaci ba.

Malamin Musulunci ya dura kan Sanusi II kan kalamansa
Sheikh Musa Yusuf Assadusunnah ya soki Sarki Sunusi II kan kiran mata su rama marin da mazajensu suka yi musu. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Sheikh Musa Yusuf Assadussuna.
Asali: Facebook

Sheikh Assadus Sunnah ya ba da shawara kan zaman aure

Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya fadi haka ne a cikin wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa rawaninku," Sarki Sanusi II ya fadi abin da ke barazana ga sarakai a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda Sarkin da ke ikirarin yana da ilimin addini zai yi wadannan kalamai inda ya ce ya ji tsoron Allah.

Malamin ya ba da shawarar a guji duk hanyar da za ta kawo abin da zai sanya miji dukan matarsa tun farko shi ne maslaha.

"Maganar da wani tsohon sarki ya yi, wani tsohon sarki daga cikin sarakunan kasar nan, ya taba fada kuma ya sake maimaitawa cewa yarsa idan mijinta ya mare ta ta rama."
"Sannan shi wannan yana danganta kansa da addini, ni dai ban kira suna ba wani tsohon sarki ne, to shi wannan sarki ya ji tsoron Allah."
"A matsayinsa na shugaba, yar da za ta je gidan miji kana mata wasiyya irin haka, me kake tsammanin zai biyo baya na matsaloli a gidan aure."

- Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah

'Annabi bai ce a bugi mata ba' - Sheikh Assadussunnah

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan 'dalilin' mamaye fadar Sanusi II, an ce hakan ka iya zama alheri

Malamin ya ce a kwanaki sarkin ya taba cewa laifin mutanenmu ne ake sace 'ya'ya zuwa Kudu inda ya ce zai hukunta duk wanda aka dauke masa 'da.

Sheikh Assadussunnah ya ce tun da shi malami ne ya je ya bincika ko Annabi Muhammad (SAW) cewa ya yi a rama idan haka ta faru.

Shehin malamin ya ce akwai hadisi ingantace da Annabi ya ce ka da ku bugi mata bayin Allah.

Sarki Sanusi II ya gargadi sarakuna kan dukan mata

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda bincike ya nuna yawan kararrakin cin zarafi a kotuna.

Mai martaba Sanusi II ya bayyana cewa masarauta ba za ta lamunci duk wani basarake da ke lakadawa matarsa duka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.