Daga Fara Aiki, Hafsan Sojojin Najeriya Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen 'Yan Lakurawa
- Babban hafsan sojojin ƙasa ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya kan barazanar ƴan ta'addan Lakurawa a Arewa maso Yamma
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba ƴan ta'addan Lakurawa za a kawo ƙarshensu a ƙasar nan
- Janar Oluyede ya nuna cewa Najeriya da ƙasashe makwabta sun huro wuta kan ƴan ta'addan domin kawar da barazanar da suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yi magana kan ƙungiyar ƴan ta'addan Lakurawa.
Shugaban sojojin ƙasan ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba ƙungiyar Lakurawa za ta zama tarihi a ƙasar nan.
Laftanar Janar Oluyede ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan wata ganawar sirri da suka yi da Bola Tinubu, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun takurawa ƴan Lakurawa
Babban hafsan sojojin ƙasan ya yi magana kan yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da sojojin ƙasashe makwabta.
"A nan Najeriya muna ragargazarsu, sannan da zarar an ba su wuta a Najeriya, suna tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar."
"Yanzu da Nijar ta huro musu wuta, hakan na nufin nan ba da jimawa ba, za a shafe tarihin ƴan Lakurawa."
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede
Oluyede ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa da ƙasashen dake makwabtaka da Najeriya, domin tunkarar barazanar da ƴan ta'addan ke yi, rahoton The Nation ya tabbatar.
"Ya kamata mu haɗa kai da ƙasashe makwabta domin su ma lamarin ya shafe su. Ta hanyar yin aiki tare, za mu iya magance barazanar yadda ya kamata."
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede
Oluyede ya kama aiki a matsayin shugaban sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan rundunar sojojin ƙasa na Najeriya, Laftajanar Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki.
Dakarun sojoji sun yi ɗan karamin biki da faretin girmamawa yayin da hafsan sojin ya shiga ofis a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a hedkwatar sojoji da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng