NNPCL Ya Fitar da Sunayen Waɗanda Suka Ci Jarabawar Ɗaukar Aikin 2024

NNPCL Ya Fitar da Sunayen Waɗanda Suka Ci Jarabawar Ɗaukar Aikin 2024

  • Kamfanin NNPCL ya fara tura sakon gayyata zuwa intabiyu ga waɗanda suka tsallake matakin jarabawar ɗaukar aiki watau CBT
  • A ƴan kwanakin da suka gabata ne NNPCL ya shirya jarabawar gwaji ta na'ura mai ƙwakwalwa watau CBT ga waɗanda suke neman aiki
  • A sakon gayyatar da kamfanin ya fara turawa waɗanda suka ci jarabawar, NNPCL ya sake nanata cewa zai soke duk wanda bai cancanta ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya fara sakin sunayen waɗanda suka kai zuwa mataki na gaba a matakan ɗaukar sababbin ma'aikata na 2024.

Wannan dai na zuwa ne bayan kammala jarabawar ɗaukar aiki wanda aka yi a na'ura mai kwakwalwa watau CBT a ƴan kwanakin nan.

Wurin jarabawar NNPCL.
NNPCL ya fara tura sakon gayyata ga waɗanda suka ci jarabawar CBT Hoto: NNPCLimited
Asali: Twitter

NNPCL ya fara tura sakon intabiyu

Tribune Nigeria ta tattaro cewa waɗanda suka tsallake zuwa mataki na gaba bayan jarabawar sun fara ganin saƙo ta akwatin tura saƙonnin imel.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fahimci halin da ake ciki, ta taso bankin CBN a gaba kan takardun kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin ya fara tura saƙonnin gayyata zuwa wurin tattaunawar baka-da-baka watau intabiyu ga waɗanda suka samu nasara a jarabawar da aka kammala.

Saƙon da NNPCL ya fara turawa

Wani sashin sakon da kamfanin NNPCL ya fara turawa mutane ya ce:

"Sakamakon samun nasara a jarabawar CBT, muna farin cikin gayyatarka zuwa mataki na gaba a tsarin ɗaukar aikin kamfanin mai NNPCL watau Intabiyu."
"Za a yi wannan intabiyu ne a hedkwatar NNPCL da ke babban birnin tarayya Abuja. Za a sanar da kai lokaci, rana da sauran abubuwan da ya kamata nan gaba."

NNPCL ya jero tsarin ɗaukar aikin 2024

Kamfanin ya jaddada cewa zai bi cancanta wajen ɗaukar aikin kamar yadda ya sanar tun da farko.

Har ila yau, NNPCL ya sake nanata cewa zai soke duk wanda aka gano ba shi da mafi ƙarancin matakin karatun da ake bukata kafin ɗaukar aikin.

Wani da ya zauna jarabawar ɗaukar aikin NNPCL, Umar Idris Dabai ya shaidawa Legit Hausa cewa ga dukkan alamu kamfanin mai ba zai duba alfarma ba a wannan karon.

Kara karanta wannan

Karfin Naira: Ƴan canji sun lissafa abubuwa 3 da suka jawo dalar Amurka ta karye

A cewar Umar, jarabawar da suka yi ba wata mai walaha ba ce kuma darasin lissafi ya fi yawa a ciki.

Matashin ya ce:

"Na zauna jarabawar a Kano, gaskiya alamu sun nuna cancanta za a bi wajen ɗaukar aiki, babu wata alfarma ko wa ka sani.
"Ni dai har yanzun ba a turo mani sakon zuwa intabiyu ba, ina wa waɗanda suka tsallake wannan matakin fatan alheri, mu ma idan da rabon mu saƙon na kan hanya."

NNPCL zai fara sayar fetur a matatar Fatakwal

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi ƙarin haske kan fetur da aka fara samarwa a matatar Fatakwal a Rivers.

Babban jami'in sadarwa na kamfanin ya bayyana cewa za a riƙa sayar da fetur ɗin ne kawai ga gidajen man kamfanin NNPCL.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262