Farautar 'Yan Daba: Kwamishinan 'Yan Sanda da Kansa Ya Shiga Unguwannin Kano
- Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kai ziyara zuwa unguwanni da dama domin magance matsalar fadan daba
- An bada umarnin gudanar da bincike da kama duk masu hannu wajen fadan daba da ya faru a unguwanni daban-daban na Kano
- Matsalar daba na ci gaba da zama barazana ga tsaro da zaman lafiya a Kano, wanda ke bukatar daukar matakan gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
jihar Kano - Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kai ziyara unguwanni da dama a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa CP Salman Dogo Garba ya yi ziyarar ne domin gano bakin zaren matsalar fadan daba da ke addabar yankunan.
Kakakin 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa yadda ziyarar ta gudana a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike tare da kama duk wanda aka samu da hannu a kan lamarin.
Fadace-fadace da matsalar daba a jihar Kano
Fadan daba yana haifar da firgici ga mazauna jihar Kano, inda mutane da dama suka rasa kadarorinsu a lokuta daban daban.
Matsalar daba tana haddasa rashin zaman lafiya a jihar Kano, inda mazauna ke fuskantar tsangwama daga ’yan daba wajen sata da kwace.
Kwamishinan 'yan sanda ya zaga unguwanni
A makon da ya wuce yan sanda suka yi wani taro domin neman hadin kai wajen kawo karshen 'yan daba kamar yadda SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.
Haka zalika a yau Litinin, 9 ga Disamba Kwamishinan 'yan sanda ya zaga unguwannin Kofar Mata, Yakasai, Rimi da Zango.
CP Salman Dogo Garba ya bada umarnin gudanar da bincike da kama duk wanda yake da hannu akan fadan daba a unguwarnin.
Gundura: An kama babban dan daba a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasara kan wasu tarin yan daba da ake zargi da aikata manyan laifuffuka.
Cikin wadanda aka kama akwai babban dan daba da ake kira da Gundura wanda shi ake zargi da jagorantar ayyukan daba a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng