'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yabi Bola Tinubu Ana Batun Kudirin Haraji

'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yabi Bola Tinubu Ana Batun Kudirin Haraji

  • Cosmos Ndukwe ya nuna jin daɗinsa kan naɗa 'yan majalisar gudanarwa ta hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC) da shugaban ƙasa ya yi
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP ya yabawa shugaba Bola Tinubu kan mutanen da ya zaɓo ya naɗa muƙamai a hukumar
  • Ya nuna cewa mutanen da aka ba muƙaman ƙwararru ne waɗanɗa za su yi amfani da gogewarsu wajen kawo ci gaban da ake buƙata a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a shekarar 2023, Cosmos Ndukwe, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon ɗan takarar ya yabawa shugaba Bola Tinubu ne kan naɗa mambobin majalisar gudanarwa ta hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC).

An yabawa Shugaba Bola Tinubu
Cosmos Ndukwe ya yabawa Shugaba Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Ndukwe, wanda ya koma jam’iyyar APC, kwanan nan, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa waɗanda aka ba muƙaman za su iya yin aikin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya samu yabo kan hukumar SEDC

Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia, ya bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin masu ƙwarewa da suke da tarihin yin aiki yadda ya dace.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shugabancinsu zai taimaka wajen magance ƙalubalen samar da ababen more rayuwa a shiyyar Kudu maso Gabas.

"Tare da gogaggun masu kishin ƙasa kuma masu hangen nesa a matsayin mambobin hukumar SEDC, babu shakka za a cimma manufofin hukumar.
"Za a cimma burin shugaban ƙasa na kawo ci gaba Kudu maso Gabas ta hanyar ƙwarewarsu da sadaukarwarsu."

- Cosmos Ndukwe

Ndukwe ya yabawa Shugaba Tinubu bisa sanya hannu kan dokar hukumar SEDC, abin da gwamnatocin baya suka kasa yi.

Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar SEDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori shugaban hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC), ƴan sa'o'i da ba shi muƙamin.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya gano kuskuren Tinubu kan kudirin haraji na gwmanatinsa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kuma maye gurbin wasu mutane huɗu da ya naɗa muƙamai a hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng