Bidiyo: Matar El Rufai Ta Shiga Tashin Hankali, Ta Gamu da Katuwar Macijiya a Gidanta
- Wasu migayun macizai, dangin 'Cobra' sun kutsa kai cikin harabar gidan Hadiza Isma El-Rufai a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba
- Legit Hausa ta rahoto cewa Hadiza, marubuciya ce kuma daya daga cikin matan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i
- Matar tsohon gwamnan ta nemi dauki yayin da ta ci karo da shirgegiyar maciya da danta amma aka gagara gano inda mijin yake
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna – Wani faifan bidiyo ya nuna wata katuwar macijiya, dangin su 'Cobra' a gidan Hadiza Isma El-Rufai, matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.
Maciji mai daƙarƙari (cobra) maciji ne mai guba wanda yake a nahiyoyin Afirka da Asiya. Ana gane shi ne da yadda yake buɗa haɓar wuyansa kamar hular rawa.
A cikin wani faifan bidiyo na daƙiƙa 18 da matar El-Rufai ta wallafa a shafinta na X a ranar Lahadi, 8 ga Disamba, an ga wasu mutane suna ɗaukar bidiyon maciji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama maciji a gidan matar El-Rufai
Legit Hausa ta fahimci cewa fiye da mutane 500,000 ne suka kalli wannan bidiyo.
Da take bayar da karin haske a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, matar El-rufai ta ce an kuma gano wani jaririn maciji, ta kara da cewa ba a samu damar kama mijin macijiyar ba.
Ta wallafa cewa:
"Mun kuma samu wani jaririn maciji. Kobra da muka kama da farko mace ce. Mai kamun macizan ya yi iya dubawarsa amma bai kama mahaifin jaririn macijin ba.
"A karshe dai zan iya cewa: Mazan macizai, kamar wasu mazan bil Adama ne. Gogan naku ya arce bayan ya gama aika aikarsa."
Kalli bidiyon a kasa:
Mutane sun yi tsokaci kan wannan bidiyo
A halin da ake ciki dai 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu bayan gano macizai a gidan Hadiza El-Rufai.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin ma'abota shafin X.
"Ki kasance cikin aminci Hajiya. Babu wani mugun abu da zai same ki. Da yanzu macijin ya sari wani. Ki sanya masu kamun maciji su bi lungu da sako na gidan su fitar maki da macizai."
"Wannan ko dai aikin mutanen kauye ne."
"SubhanalLah. Hajiya, ki kula sosai don Allah. Muna addu'ar Allah ya tsareki da iyalanki. Amin."
Matar El-Rufai ta ci gyaran Shehu Sani
A wani labarin, mun ruwaito cewa matar Malam Nasir El-Rufai, Hajiya Hadiza ta fito ta ci gyaran turancin Sanata Shehu Sani a wani rubutu da ya yi a kwanakin baya.
Sai dai wannan gyaran turanci da Hajiya Hadiza ta yi, ya kona ran Sanata Shehu Sani, inda ya bukaci matar tsohon gwamnan na Kaduna da ta fita daga harkokinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng